Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Annobar amai da gudawa ta ɓarke a unguwar Hotoron Walawai

Published

on

Al’ummar unguwar Hotoro walawai da ke ƙaramar hukumar Tarauni anan Kano sun koka kan yadda annobar Amai da gudawa ta ɓarke a unguwar lamarin da ke barazana ga lafiyar su da rayuwar su.

Sai dai sun ce ɓarkewar cutar na da nasaba da wani ruwan famfo da suke amfani da shi a unguwar.

Annobar kwalara dai da ta ɓarke a unguwar Hotoro Walawai inda ta jikkata al’ummar yankin da dama, har ma suka bayyana cewa cutar ta zo musu a bazata.

Wasu ƴan unguwar sun ce “cutar na da nasaba da yadda suke shan wani ruwa,wanda ya ke dab da bola tare da shan sa a haka, sannan sun bayyana cewa wani lokacin ruwan kan sauya kala”.

Mazauna unguwar ta walawai sun kuma ce “ɓarkewar amai da gudawar yayi sanadiyyar jikkata wasu daga cikin ƴaƴansu tare da rasa rayuka da dama, wanda a kowanne gida akan samu sama da mutane hudu na fama da cutar”.

Aminu Dauda Adam shi ne mai unguwar Hutoro walawai ya ce “Na samu labarin ɓarkewar annobar sakamakon koken da mutane suke yi”.

“Gwamnati ta taimaka mana musamman ma ama’aikatar lafya wajen kawo mana ɗauki”.

Sai dai a ƙoƙarin da Freedom Radio ta yi na jin ta bakin ma’aikatar lafiya ta jihar Kano musamman ma ma’aikatar lafiya don jin ƙoƙarin su kan annobar da ta ɓarke a unguwar ta Walawai, sai dai duk kiran da muka yi wa sashin da ke kula da cututtuka masu yaduwa na ma’aikatar ba su amsa ba.

Za mu ci gaba da bibiyar mahukuntan da abun ya shafa domin jin wanne tallafi suka kai wannan unguwar ta Hotoro Walawai.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!