Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

NBC ta yanka wa Channels Tv tarar miliyan 5

Published

on

Hukumar kula da kafofin yaɗa labarai ta Nijeriya NBC, ta ci tarar gidan talabijin na Channels har Miliyan biyar sakamakon karya doka a wani shiri da suka gabatar tare da ɗan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Dakta Datti Baba-Ahmed.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata wasiƙa da shugaban hukumar Balarabe Illela, ya sanya wa hannu tare da aikawa shugaban gidan talabijin ɗin.

Wasikar mai ɗauke da kwanan watan 27 ga watan Maris an ta bayyana ne a ranar 31 ga watan na Maris.

Haka kuma, ta cikin wasiƙar, Balarabe Illela, ya ce, hukumar ta NBC ta lura da yadda aka haska wata hira kai tsaye da mataimakin ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Dakta Datti Baba-Ahmed, da mai gabatar da shirin harkokin siyasa Seun Okinbaloye, a ranar Laraba, 22 ga watan Maris inda a cikinta aka yi kalaman da suka saɓa ƙa’ida.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!