Labarai
NAHCON za ta fara hukunta masu karbar kudi fiye da kima a wurin maniyyata
Hukumar aikin hajji ta Najeriya NAHCON ta bayyana shirin da take yi na soma hukunta hukumomin jin daɗin alhazai a jihohin ƙasar, da ke karɓar fiye da kuɗin kujerar hajj da hukumar hadin gwiwa da hukumomin suka ƙayyade.
Cikin sanarwa da mataimakin daraktan yaɗa labarai na hukumar ta NAHCON, Musa Ubandawaki ya sanyawa hannu, hukumar ta ce kuɗin hajjin bana da ta sanar ranar Juma’ar da ta gabata bai sauya ba.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa har yanzu farashin kujerar Hajji tana kan ƙasa da naira miliyan uku.
Sanarwar ta kuma gargaɗi duk wata jiha da ke tatsar maniyyatanta, za ta iya rasa lasisinta ko ma rasa kason kujerun hajjin da aka ware mata ba tare da ɓata lokaci ba.
Rahoton: Ahmad Kabo Idris
You must be logged in to post a comment Login