Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Bola Tinubu ya ce ‘yan Nijeriya su kara hakuri

Published

on

Shugaban kasar Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya ce al’ummar kasarnan zasu ji dadi nan gaba, bayan kalubalen da suke fuskanta a halin yanzu sanadiyyar janye tallafin man fetur.

Bola Tinubu ya bayyana hakan ne jiya Alhamis a yayin taron tunawa da Edwin Clerk, wanda sakataren gwamnatin tarayya George Akume ya wakilta.

Ya ce radadin da yan Nigeria ke fuskanta sanadiyyar janye tallafin dai-dai yake da radadin da mata masu juna biyu ke fuskanta yayin haihuwa, a don haka radadi ne na haihuwar sabuwar Nigeria da yan kasar zasuyi alfahari da ita a nan gaba.

Koda yake shugaba Tinubu ya ce matsalolin kasarnan ba wadanda za’a iya magancewa bane nan take, saidai suna bukatar hada karfi da karfe da kowanne dan kasa domin magance su.

 

Rahoton: Mukhtar Abdulkadir Birnin Kudu

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!