Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnatin tarayya ta amince da bada Biliyan 5 ga gwamnonin kasar nan

Published

on

 

Majalisar Tattalin Arziki ta Nijeriya (NEC) ta amince da bayar da Naira Biliyan 5 ga kowace Jiha a matsayin tallafi don rage radadin cire tallafin man fetur.

An dauki wannan matakin ne a zaman majalisar da aka yi a ranar Alhamis a karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima wanda gwamnonin jihohi da sauran mambobin majalisar suka halarta a fadar gwamnati da ke Abuja.

Idan za a iya tunawa, a ranar 29 ga watan Mayu ne shugaban kasa Bola Tinubu a jawabinsa na rantsar da shi ya sanar da kawo karshen bayar da tallafin man fetur.

Daga cikin gwamnonin da suka halarci taron akwai Abdulrahman Abdulrazak (Kwara), Hope Uzodinma (Imo), Inuwa Yahya (Gombe) Dauda Lawal (Zamfara), Dr. Alex Otti (Abia), Babajide Sanwo-Olu (Lagos) da Ademola Adeleke (Lagos).

Sauran sun hada da Sanata Bala Mohammed (Bauchi), Sanata Uba Sani (Kaduna), Sheriff Obrevwori (Delta), Charles Soludo (Anambra), Godwin Obaseki (Edo), Yahaya Bello (Kogi), Umaru Namadi (Jigawa),

Haka kuma a taron akwai Gwamna Umo Eno (Akwa Ibom), Prince Bassey Otu (Cross River), Lucky Aiyedatiwa (Mukaddashin Gwamnan Jihar Ondo), Dapo Abiodun (Ogun), Ahmad Aliu (Sokoto), Agbu Kefas (Taraba), Abdullahi Sule. (Nasarawa), Peter Mbah (Enugu), Babagana Zulum (Borno)

Mataimakan gwamnonin jihohin Katsina, Ribas, Yobe, Adamawa, Kano, da Kebbi duk suma sun halarci taron.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!