Labarai
Rike al’adun gargajiya ne zai tsiratar da lalacewarsa a cikin al’umma: Sarkin Kano
Mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci al’ummar kasar nan dasu cigaba da rike al’adunsu na gargajiya duba da yanda al’adunsu suke neman lalacewa.
Sarkin ya bayyana haka ne lokacin daya karbi bakoncin shugaban kungiyar Big Break Moment African Tayo Folorunsho da Yan tawagarsa suka ziyarar ce shi a fadar sa.
Alhaji Aminu Ado Bayero yace ‘wannan ziyara tana da matukar mahimmanci duba da yanda zasu ga yanda al’adun a jihar Kano suke.
A nasa jawabin shugaban kungiyar Big Break Moment yace yaji dadin wannan ziyara daya kawo Kano, Wanda hakan zai bayar da damar kulla alaka da daliban jami’oin jihar.
Freedom Radio ta rawaito cewar bakin sunyi alkawarin mai da hankali wajen bunkasa al’adun gargajiya cikin al’amuran su na yau da kullum.
Rahoton: Shamsu Da’u Abdullahi
You must be logged in to post a comment Login