Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ya kamata likitocin asibitin kashi na Dala su rage kudade ga marasa lafiya: Sarkin Kano

Published

on

Mai  martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya tunatar da asabitin  kashi na dala kan su kula da tsarin ayyukansu wajen tausayawa marasa lafiya, ta hanyoyin rage musu kudaden magani a asibitin, don ragewa al’umma radadin da suke ciki.

Sarkin yayi wannan kira ne lokacin da ma’aikatan asibitin kashi na dala karkashin jagorancin sabon shugaban asibitin Dakta Nuraddeen isah suka ziyarce shi a fadar sa.

Alhaji Aminu Ado Bayero yace, “duba da yanda al’umma suka samu kai a ciki na rashin kudi da sauran wahalalu ya kamata suyi duba da hakan wajen rage kudin magani a asibitin”.

A nasa jawabin Sabon shugaban asibitin Dakta Nuraddeen Isah ya tabbatarwa da sarkin cewa, “zasu fidda sabon tsarin da zai taimakawa marasa lafiya, tare kuma da yin amfani da motocin da asibitin ya samar don dauko marasa lafiya”.

Freedom Radio ta rawaito cewa Sabon shugaban asibitin kashi na dala yace ‘sun horar da likitoci daban-daban don kula da lafiyar al’umma da kuma magance fita kasashen ketare don neman lafiya’.

 

Rahoton: Shamsu Da’u Abdullahi

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!