Labarai
Matatar Mai ta Fatakwal ta fara aiki
Matatar Mai ta Fatakwal da ta dade ba ta aiki kamar sauran matatun mai da gwamantin Najeriya ta jima tana kashe kudi domin farfaɗo da su ta fara aiki a yau Alhamis.
Haka zalika gwamantin Najeriya ta jima tana kashe kudin domin farfaɗo da su, wadda ta Fatakwal din na Daya daga cikinsu, ta Kuma tashi bayan aikin gyaran da akayi mata tun a tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari.
Rahotanni sun nuna a safiyar Alhamis ne aka ga matatar mai karfin tace ganga 210 na danyen mai a kullum ta fara aiki.
Sai da tsohon Shugaban Kungiyar Dillalan Mai Na Najeriya (IPMAN) a Jihar Ribas, Joseph Obele, ya shaida wa manema labarai cewa ”yanzu an kammala kashin farko na gyaran matatar man, kuma an fara aikin gwaji, wand ake cigaba da gwajin ta.”
A baya dai an yi ta ce-ce-ku-ce bayan da masu ruwa da tsaki suka bayyana shakka game da yiwuwar kammala aikin gyaran matatar a watan Disambar nan.
A wata ziyarar gani da ido da ya kai matatar, Karamin Ministan Man Fetur, Heineken Lokpobiri ya bayyana cewa ‘yana da kwarin gwiwa za a kammala kashin farko na aiki a cikin watan Disambar.
You must be logged in to post a comment Login