Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Matatar Mai ta Fatakwal za ta fara aiki a Disamba- Tinubu

Published

on

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar da cewa matatar Mai ta birnin Fatakwal za ta fara aiki nan da watan Disamban bana.

Shugaba Tinubu ya tabbatar da hakan ne yayin da ya ke ganawa da shugabannin kungiyar kwadago.

Wata sanarwar hadin gwiwa da shugabannin kungiyar kwadago ta NLC Joe Ajaero da takwaransa na Trade Union Congress, Festus Osifo suka fitar a daren jiya Laraba, ta cewa, batun fara aikin jmatatar na cikin muhimman batutuwan da suka tattauna da shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda kuma ya dauki wasu alkawura da dama da hakan ta sanya su amincewa da komawa kan teburin tattaunawa don samun mafita.

Kungiyoyin kwadagon, sun kuma yaba wa ‘yan Najeriya bisa nuna goyon baya ga zanga-zangar lumana da suka yi a jiya Laraba tare dashan alwashin cewa sun zuba ido wajen ganin gwamnatin tarayya ta yi abinda ya dace kan rage farashin Man fetur.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!