Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tinubu zai saka kafar wando daya ga duk wanda zai kawo tarnaki ga tsaron Nijeriya

Published

on

Shugaban kasar Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya lashi takobin sanya kafar wando daya da duk wanda aka samu da hannu wajen yiwa kokarin da sojojin kasarnan ke yi na magance matsalolin tsaro kafar angulu.

‘Haka kuma ya gargadi rundunonin tsaron kasarnan bisa yadda ake samun yawaitar kaiwa fararen hula hari bisa kuskure, inda ya ce gwamnatin sa ba zata lamunci hakan ba’.

Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a yammacin jiya Juma’ah, yayin da yake nuna alhinin sa game da hare-haren da yan ta’adda suka kai a baya bayan nan, ciki har da wadda aka kai yankin unguwar Kwari ta karamar hukumar Gaidam a jihar Yobe, da kuma wadda yayi sanadiyyar rasa rayukan yan kasuwa 6 a yankin karamar hukumar Danmusa ta jihar Katsina.

Rahoton: Mukhtar Abdullahi Birnin Kudu

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!