Labarai
Abdulaziz Yar’Adua ya zama shugaban kungiyar Sanatocin Arewa
Sanatocin yankin Arewacin Nijeriya, sun nada wakilintar Katsina ta tsakiya Sanata Abdulaziz Yar’Adua a matsayin sabon shugaban kungiyar Sanatocin Arewa.
Nadin nasa dai ya biyo bayan murabus din da shugaban kungiyar Sanata Abdul Ningi, mai wakiltar Bauchi ta tsakiya ya yi.
Tun da fari dai Majalisar dattijai ce dai ta dakatar da Ningi na tsawon watanni uku saboda furucin da ya yi kan zarge-zargen a kasafin kudin 2024.
Ningi, a wata wasika da ya aike wa kungiyar, ya rubuta cewa, “Ina so in ajiye mukamina na shugaban kungiyar Sanatocin Arewa. Tabbas hakan ya zama dole saboda abubuwan da ke faruwa a Majalisar Dokoki ta Kasa da Arewa da ma kasa baki daya.”
Haka kuma, kungiyar ta bayyana Sanata Tahir Mungono mai wakiltar Borno ta Arewa a matsayin mai magana da yawunta da zai maye gurbin Sanata Sumaila Kawu wanda majalisar ta gargadi shi da ya daina raba mukamai da za su iya haifar da tarzoma a kasar.
You must be logged in to post a comment Login