Kasuwanci
Ƴan Kwari sun yi barazanar kulle kasuwar

Wasu ƴan kasuwar Kantin Kwari, sun yi barazanar kulle kasuwar matukar gwamnatin Kano ba ta mayar musu da ofishin jami’an kashe gobara na kasuwar da suke zargin an sayar da shi ba.
Yan kasuwar sun yi wannan ikirari ne yayi wani taron manema labarai da suka gudanar.
Da dama daga cikin kungiyoyin yan kasuwar da kuma shugabanin kungiyoyin gidaje ne suka fito domin nuna kin amincewar su kan wannan lamari.
A ganawarsu da manema labarai, sun ce ba ya ga offishin jami’an kashe gobarar, akwai wani sabon haraji da aka kakaba musu a kasuwar wanda har yanzu sun kasa sannin dalilin sa.
Alhaji IShaq Alkasim Tatari, Shi ne shugaban kungiyar gamayyar kungiyar shugabanin gidajen kasuwar ta Kantin Kwari, ya ce akwai ta kaici yadda suke da kyakyawan zato akan wannan gwamnatin sai gashi irin wadan nan abubuwa suna tasowa.
A nasa ɓangaren, Shugaban kungiyar yan kasuwa mazauna gidan Alaramma Alhaji Yusuf M. Yusuf cewa ya yi offishin kashe gobara a kasuwar kantin kwari ya wuce guda daya ga shi kuma dayan ma ana kokarin salwantar da shi.
Da ya ke martani kan zarge-zargen shugaban kasuwar Alhaji Hamisu Sa’adu Dogonnama ya ce, ba sayar da offishin aka yi ba illa kawai ana yi masa kwaskwarima ne ta yadda za a samu tsaro da fadada kasuwanci a kasuwar.
Sai dai a nasu bangaren hukumar tsara birane ta Kano KNUPDA da hukumar karbar korafi da yaki da cin hanci da rashawa ta Kano, sun dakatar da wannan aikin domin lalubo bakin zaren.
You must be logged in to post a comment Login