Labarai
PDP ta kafa kwamitin da zai magance mata rikicin cikin gida

Jam’iyyar adawa ta PDP, ta kafa kwamitin da zai kawo ƙarshen matsalar rikicin cikin gida da ta ke fuskanta.
Jam’iyyar ta bayyana daukar wannan mataki ne bayan gudanar da taron masu ruwa da tsaki, da ta gudanar a baya-bayan nan.
Wannan lamari dai na faruwa ne yayin da Ministan birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike ke ƙalubalantar jam’iyyar wajen bayar da tikiti a shiyyar Arewacin kasar nan.
Wannan dai na zuwa ne yayin da bangaren dan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar a zaben shekarar 2023 Atiku Abubakar ke zargin cewa akwai wasu gwamnoni da suke taka rawa wajen goya wa Minista Wike baya, wajen haddasa rikicin cikin gida a jam’iyyar.
You must be logged in to post a comment Login