Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Rikicin cikin gida: Jam’iyyar PDP ta kori Aminu Ringim

Published

on

Jam’iyyar PDP reshen jihar Jigawa ta kori tsohon dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar Alhaji Aminu Ringim sakamakon zarginsa da laifukan cin amanar jam’iyya.

Shugaban jam’iyyar ta PDP a jihar Jigawa Alhaji Ibrahim Babandi ne ya sanar da korar yayin wani taron manema labarai yau a Dutse babban birnin jihar.

Ya ce tun farko Alhaji Aminu Ringim an gayyace shi domin ya bayyana gaban kwamitin da jam’iyyar ta kafa don ya kare kansa saboda zargin da ake yi masa na cin amanar jam’iyya, amma bai bayyana gaban kwamitin da jam’iyyar ta kafa ba.

‘‘Yadda abin ya ke shine, a makwanni uku da suka gabata mun karbi wasika daga mazabar Aminu Ringim da ke cewa an dakatar da shi sakamakon zarginsa da cin amanar jam’iyya’’

‘‘Saboda haka jam’iyya ta kafa kwamitin gaggawa wanda kwamitin ya gayyace shi don kare kansa game da zargin da ake yi masa, amma ya kasa bayyana saboda haka mu ka ga bamu da zabi da ya wuce mu koreshi daga jam’iyya’’. A cewar Alhaji Ibrahim Babandi.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!