Labarai
Goodluck Jonathan ya sauka a Abuja bayan dakko shi daga Guinea-Bissau

Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan, ya dawo Najeriya inda ya sauka a birnin tarayya Abuja bayan da aka fito da shi daga ƙasar Guinea-Bissau sakamakon juyin mulki da sojoji suka yi a kasar.
Rahotonni sun bayyana cewa, an dauki matakin gaggawa na dawo da shi gida Najiriya ne daga ƙasar domin tabbatar da cikakkiyar tsaronsa, yayin da rikicin siyasa ya taƙaita zaman lafiya a birnin na Bissau.
A halin yanzu dai , hukumomi na ci gaba da bibiyar al’amura domin tabatar da tsaron ’yan Najeriya da sauran jami’an diflomasiyya da ke ƙasar.
You must be logged in to post a comment Login