Labarai

Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya amince da rage lokutan aiki ga ma’aikatan gwamnati a watan Ramadan daga karfe 8 na safe zuwa 2 na rana maimakon 8 na safe zuwa 4 na yamma.
Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwar da Shugaban ma’aikatan gwamnatin Jihar Isa Ardo Shehu ya fitar.
Sanarwar ta bayyana cewa sauyin ya shafi dukkan ma’aikatan gwamnati a fadin jihar, domin bai wa ma’aikata damar gudanar da azumin watan Ramadan cikin sauki.
Gwamnan Amadu Umar Fintiri ya taya al’ummar Musulmi murnar shiga watan Ramadan tare da yi musu fatan alheri.
You must be logged in to post a comment Login