Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnatin Jigawa ta rage wa ma’aikata lokacin aiki

Published

on

Gwamnatin jihar Jigawa ta rage awanni biyu cikin lokacin aiki na ma’aiakata a fadin jihar, a wani mataki na kyautata musu a cikin watan Ramadan.

Hakan na cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban ma’aikatan jihar Hussaini Kila, wadda mai magana da yawunsa Ismail Dutse ya raba wa manema labarai.

Sanarwar ta ce, ma’aikatan jihar za su rika zuwa aiki da karfe 9:00 na safe sannan su tashi da misalin karfe 3:00 na yamma, a tsakanin ranakun Litinin da Alhamis maimakon karfe 5 na yamma.

Sannan ma’aikatan za su rika zuwa aiki ranar Juma’a da ƙarfe 9:00 na safe kuma za su tashi ƙarfe 1:00 na rana kamar yadda aka saba.

A cewar sanarwar, an rage tsawon awannin aikin ne da nufin samar da dama ga ma’aikatan gwamnati domin su yi ibada a watan Ramadan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!