Labarai
Da misalin karfe 7:46 na safiyar Litinin din nan ne wasu ‘yab bindiga da ba’a kai ga gano su ba, suka yi garkuwa da mai kula da aikin Titin Ring Road mai suna Mike wanda kuma farar fata ne, da yake aiki da kamfanin Dantata and Sawoe wanda ke tsaka da gudanar da aikin ginin titin na Ring Road a nan Kano.
Mutanen su 3 sun je wurin ne a cikin wata mota kirar Golf baka, zuwan na su ke da wuya sai suka fara harbi a sama tare da farwa jami’in dan sandan da ke kula da ma’aikacin kamfanin, a dai dai lokacin da yake cikin mota har sai da suka ga ya daina numfashi.
Wasu da lamarin ya faru a kan idanunsu sun yi wa gidan Rediyo Freedom karin haske dangane da faruwar lamarin.
Abubakar Sani Muhammad shi ne mai gadin kayan aikin titin kamfanin na Dantata and Sawoe, kuma daya ne daga cikin wanda abun ya faru a kan idonsa, ya yi mana karin haske dangane da faruwar lamarin.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan-sandan Jihar Kano SP Magaji Musa Majiya ya tabbatar mana da faruwar lamarin, inda ya ce nan gaba kadan za su fitar da cikakken rahoto kan abinda ya faru.
Wakilinmu da ya halarci wajen ya ruwaito mana cewa masu garkuwa da mutanen sun yi awon gaba da Bindigar jami’in dan-sandan da ke kula da lafiyar Mike din.