Connect with us

Labarai

Kano: An yi harbe-harbe a titin gidan Zoo

Published

on

Harbe-harben ƴan bindiga ya tarwatsa jama’a a titin gidan Zoo, daidai Ado Bayero Mall da ke nan Kano.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10 na daren Asabar.

Ƴan bindigar sun riƙa harbi sama wanda hakan yayi sanadiyyar yin gudun tsira ga jama’a.

Daga nan ne kuma suka nufi wani mutum da ke cikin mota inda suka fitar da shi ta ƙarfi tare da harbinsa.

Sannan suka yi awon gaba da motar ta sa kamar yadda wani shaidar gani da ido ya shaida wa Freedom Radio.

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin jami’in yaɗa labaranta DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa.

Ya ce, jami’ansu sun kai ɗauki wurin bayan da suka ji ƙarar harbe-harben, kuma a yanzu haka sun kai wanda aka harba asibiti.

Ƴan sanda sun ɗauko motar da ƴan bindigar suka tafi da ita, bayan da suka arce suka barta, saboda ganin ƴan sanda za su cin musu a cewar Kiyawan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,433 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!