Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Amnesty ta zargi mahukuntan Najeriya da rashin kyautatawa matan da suka tsere daga yankunan da Boko Haram ya daidaita.

Published

on

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta zargi hukumomin Najeriya da rashin kyautatawa dubban matan da suka tsere daga yankunan da rikicin Boko Haram ya daidaita.

Zargin na kunshe ne cikin sanarwar da kungiyar ta fitar akan ranar mata ta duniya.

Rahoton Amnesty ya ce da dama daga cikin matan nan na shan wahala kafin samun abinci da sauran abubuwan more rayuwa a sansanonin ‘yan gudun hijirar da suke rayuwa a ciki, duk da takaita musu zirga-zirga.

Rashin samun kulawar da yakamata da takaita zirga-zirga na sa matan fuskantar cin zarafi daga jami’an hukumomin tsaro da ke ciki da wajen sansanonin.

Daraktan kungiyar Amnesty International, Osai Ojigho, ya ce; hana matan da suka fuskanci hare-haren Boko Haram hakkokin su ya sabawa ka’ida. Kuma a cewar Ojigho, jami’an tsaron sun dade suna cin zarafin mata a madadin abincin da suke basu, don su ciyar da kansu da kuma ‘ya’yan su.

Daraktan ya kara da cewa ko a shekarar da ta gabata sun fitar da rahoton da ke nuna yadda jami’an tsaro ke yi wa mata fyade da kuma barin su a cikin yinwa, sai dai gwamnati ta yi watsi da binciken.

Binciken na Amnesty Inernational ya kuma nuna cewa da dama daga cikin matan suna gab da fidda tsamanin samun adalci ganin yadda aka dade ana daukar musu alkawari ba tare da an cika ba.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!