Connect with us

Labarai

Majalisar zartarwa ta amince da a gina sabbin makarantu 7 a shiyyoyin Najeriya

Published

on

Majalisar zartarwa ta kasa ta amince da a gina sabbin makarantu guda bakwai a kowanne daga cikin shiyyoyin kasar nan harda da birnin tarayya Abuja.

Ministan yada labarai da raya al’adu Alhaji Lai Mohammad ne ya sanar da hakan bayan kammala taron majalisar zartaswar ta kasa, jiya Alhamis a Abuja.

Makarantun da za a gina a Jihohin Imo da Katsina da Edo da Bauchi da Lagos da Nassarawa da kuma birnin tarayya Abuja za su lakume naira biliyan hudu da miliyan dari shida.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!