Labarai
Majalisar dokokin Kano zata kirkiro sababbin sarakunan gargajiya
Majalisar dokokin jihar Kano ta bukaci kwamitin ta da ke kula da kananan hukumomi da sarautun gargajiya da ya dauko dokar sarautar gargajiya ta jihar ta Kano domin nazarin kan yiwuwar kafa sabbin sarakunan yanka masu daraja ta daya a jihar.
Hakan ya biyo bayan karanta wata wasika da wani ofishin lauya mai suna Ibrahim Salisu chambers ya aikowa majalisar; wanda ya bukaci kafa sabbin masarautu a kananan hukumomin Rano da Gaya da Karaye da kuma Bichi.
Yayin tattauna batun mabobin goma sha uku da suka bada gudunmawa sun goyi bayan dauko dokar domin nazarin ta a gobe Talata.
Sai dai ya yin zaman majalisar na yau mamba mai wakiltar karamar hukumar Gezawa Isyaku Ali danja ya fice daga zauren, yana mai zargin takwarorinsu da sa siyasa cikin lamarin.
Da ya ke kare matakin da suka dauka kan batun, shugaban masu rinjaye na majalisar Baffa Babba Dan-Agundi ya ce babu batun siyasa cikin Matakin da suka dauka.
majalisar ta umarci kwamitin da ya kawo dokar a gobe talata.