Connect with us

Kasuwanci

Majalisar dattawa ta amince a biya wasu kamfanoni kudaden tallafin mai

Published

on

Majalisar dattawa ta amince da a biya wasu kamfanoni 67 kudaden tallafin mai da ya kai naira biliyan 129.

Hakan ya biyo bayan amincewa da rahoton kwamitin kula da albarkatun man fetur wanda Sanata Kabiru Marafa ke jagoranta.

Wannan dai shi ya kawo jimillar naira biliyan 545 da miliyan 900 wanda majalisar dattawa ta amince da a biya dillalan na mai kudaden tallafin tun daga watan Yulin bara zuwa bana.

Haka zalika majalisar ta bukaci gwamnatin tarayya da ta biya dukkannin sauran kudaden tallafin mai domin kawo karshen shirin baki daya.

Kasuwanci

Wasu ‘yan kasuwar Sabon gari sun koka kan yunkurin Uba Zubairu

Published

on

Wasu ‘yan kasuwa dake gudanar da harkokin kasuwancin a filin parking na Muhammadu Abubakar Rimi wato Sabon Gari anan Kano, sun koka dangane da yunkurin tashin su da suka ce shugabannin kasuwar na kokarin yi.

‘Yan kasuwar dai sun ce shugabannin kasuwar karkashin Uba Zubairu Yakasai, ya aike da wani mutum rike da abar magana yana cewa su tashi daga kasuwar nan da mako daya.

Sun kuma shaidawa Freedom Rediyo cewar shakka babu za su fada cikin mawuyacin hali idan aka tashe su.

Alhaji Abba Muhammad na zaman daya daga cikin shugabannin leburorin da suke aiki a wajen, ya bayyana cewa kasancewar dayawa daga cikin su masu kananan karfi ne, idan har aka tashe su basu san inda za su zauna don gudanar da kasuwancin su ba.

Da yake jawabi, daraktan mulki na kasuwar Muhammad Bashir Abdul Durumin Iya, ya ce Gwamnatin jihar Kano ce ta bayar da umarnin tashin su don za tayi amfani da wajen.

‘Yan kasuwar sun bayyana mana kafar mu cewar, mutanen dake kasuwanci a wajen sun doshi sama da dubu uku.

Continue Reading

Kasuwanci

An fara kera Fensir a Najeriya

Published

on

Wani kamfani a nan  gida Najeriya ya fara kera fensira ta hanyar amfani da tsaffin jaridu .

 

Ministan kimiyya da fasaha Dr. Ogbonnaya Onu ne ya bayyawa cewar kamfanin zai fara samar da akalla pensira fiye da miliyan biyu a duk shekara wanda ya fi karfin amfani birane da yankuna kadai.

 

Da yake Magana jiya a Abuja yayin da ya karbi bakuncin gangun wani kamfanin da ke samar da pensira na Bamib ya ce’ mun yaba da yadda kake gudanar da ayyukanka na cigaban kasa.

 

Ya ce a wata ziyara da suka kai wani kamfanin samar da fensira a jiha Enugu , ‘mun tarar da su suna gudanar da bincike akan fensira, abin takaici ne sakamakon kasar nan bata da wani kamfani da ke samar da fensira a Najeriya .

 

A da akwai wasu kamfanunuwa da suke sarrafa fensira amma dukkaninsu sun dakushe a yanzu, hakan ce ta sa a matsayina na ministan kimiyya da fasaha na ga dacewar sarrafa shi a Najeriya duba da yadda daliban mu na firamare da ma wasu yan sakandare da ke amfani da fensir.

 

Minister Onu ya ce a ganinsa fensir ba wani a zo a gani ba, ya kuma zama wajibi a ce Najeriya tana samar da fensiran da take amfani da su.

 

Ya ce mun basu shekara biyu domin samar da adadin fensiran da ake bukata, yana mai cewa samar da fensiran ya dauki hankali na, domin kuwa duk kayayyakin da ake kera fensiran muna da shi a Najeriya, hakan dai zai samar da ayyukan yi ga matasa

 

Ministan ya ce kawo yanzu an samu cigaba domin zasu tabbatar da cewar an samar da dukkanin kayayyakin a nan gida Najeriya, tare da cewar tuni gwamnatin Akwa Ibom suka fara kira fensira wanda wannan wani cigaba ne.

Continue Reading

Kasuwanci

Kamfanin TCN ta tallata gwanjon jirage masu saukar ungulu

Published

on

Jirgi mai saukar ungulu

Bayan shafe shekaru na halin ko in kula da kamfanin samar da  wutar lantarki ta kasa ,wanda ta gada daga tsohowar kamfanin wutar lantarki NEPA na wasu  jirage masu saukar ungulu guda hudu, wanda kudadensu ya kai kimanin dala dubu dari bakwai da ashiri kwatankwacen fiye da Naira miliyan dari biyu da hamsin da biyu, wanada za’a yi gwanjon  su.

 

Jiragen mallakin hukumar samar da wutar lantarki ta  sun bayyana kudirinsu na gwanjon wadannan jirage mai kirar BO-105 , da suke ajeye a filin jiragen saman na cikin gida dake Murtala Muhammad a jihar Lagos.

 

Jaridar Punch ta rawaito cewar jiragen saman masu saukar ungulu da ake amfani da su wajen kai kawon duba kayyakin wutar lantarki tare da aiwatar da wasu gyare-gyare a fadin kasar nan , suna nan zaune ne ba tare da ana amfani da su ba na tsawon lokaci.

 

Biyu daga cikin jiragen masu dauke da lamba 5N-ASK da 5N-ASJ rabon da suyi yi aiki tun a shekara ta 1995-1997, kuma an kira su ne a  shekara 1978.

Kamfanin TCN ya ce wasu kwantenoninsa guda biyu sun yi batan dabo

Kamar yadda hukumar samar da wutar lantarkin  ta ce, babu fa’ida na a gyara su, mai makon haka, kamata yayi a sayar da su a akan kudi dala dubu dari a halin da suke ciki.

 

Ragowar jiragen kuwa guda biyu masu lambar ta rijista 5N-BCj da 5N-EPA suna ajeye ne tun shekara ta 2008 kuma za’a iya sayar da su a kan kudade dala dubu dari uku da arbain da kuma dala dubu dari da tamanin.

 

Su kuma an kira su ne a shekara ta 1996 da kuma 1993 suma gyara wanda za’a iya gyara su domin suyi aiki amma na dan lokaci.

 

Hukumar dai a ‘yan kwanakin nan ne suka fitar da gayyatar masu saye domin su zo su saye.

 

A dai kwanakin baya ne  tawagar gwamnati daga  bangaren sharia suka je suka duba jiragen masu saukar ungulu a ranar Asabar din da ta gabata domin duba su kafin a fara gwanajan su.

 

Haka zalika Shugaban  kwamitin majalisar datijjai dake kula da wutar lantarki sanata Yusuf Yusuf dake wakiltar Taraba ta tsakiya ya ce makasudin ziyarar shi ne  domin duba lafiyar jiragen  kafin a sayar da su.

 

Ya kara da cewa daga cikin abinda suka gani za’a yi iya gwanjon biyu daga cikin su , amma ragowar kuwa za’a iya sayar da su a matsayin ‘yan gwangwan

Continue Reading

Now Streaming

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!