Labarai
Kamfanin TCN ya ce wasu kwantenoninsa guda biyu sun yi batan dabo
Kamfanin tunkudo wutar lantarki na kasa TCN ya ce wasu kwantenoninsa guda biyu da ke dauke da kayayyakin lantarkin sun yi batan dabo a wasu tashoshin jiragen ruwan kasar nan.
Manajan darakta kamfanin na TCN Usman Gur Muhammad ne ya bayyana hakan a jiya Laraba yayin zantawa da manema labarai a Abuja, yana mai cewar guda daga cikin kwantenoni 775 da aka gano babu komai a cikinta.
Usman Gur ya shaida cewa kamfanin ya cimma matakin karfin lantarki da Yammacin Afirka da aka tsayar, kuma yana kan hanyarsa kara bunkasa wutar da akalla megawatt 2000 zuwa 3000.
Ya kuma kara da cewa duk da dimbin jarin da kamfanin ke zubawa tare da tunkudo wutar, to amma kamfanonin rarraba wutar wato DisCos sun gaza wajen daidaituwa da TCN din musamman fannin inganta kayayyakin aikinsu.
Kuma hakan na kawo nakasu ga samar da isasshiyar wutar lantarkin a kasar nan.