Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

APC zata daukaka kara kan shari’ar zaben gwamnan Sokoto

Published

on

Jami’yyar APC a jihar Sokoto ta bayyana cewa bata gamsu da hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe ta gudanar a jiya ba, wacce ta kori karar da dan takarar jam’iyyar APC Ahmad Aliyu ya shigar yana kalubalantar zaben gwamna Aminu Waziri Tambuwal

 

Wannan na kunshe a wata sanarwa da Shugaban jamiyyar APC, na jihar Sokoto Alhaji Isa Acida ya fitar a yau.

 

Jamiyyar ta bayyana cewa bata amince da hukunci da kotu sauraron kararrakin ta yi ba, a cewar sa kotun ta nuna son kai da bangaranci.

 

Ya kara da cewa lauyoyin na nan na bincike kan bayanan da kotun ta fitar, sannan zasu daukaka kara a kotun da ya dace.

 

Shugaban jamiyyar ya kuma kira ga yan jamiyyar ta APC a duk fadin jihar da su kara hakuri su kuma zauna lafiya, tare da tabbabar musu da cewar jamiyyar zata yi iya kokarinta.

 

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!