Connect with us

Labaran Wasanni

An fara gasar Ahlan Cup a Kano

Published

on

A jiya Lahadi ne aka bude gasar cin kofin shugaban hukumar kwallon kafa ta jihar Kano Alhaji Shariff Rabiu Inuwa Ahlan karo na uku a filin wasa na Sani Abacha dake Kano.

Manyan kungiyoyin kwallon kafa a Nigeria ne zasu fafata a gasar wadda aka raba zuwa rukuni hudu.

Rukunin A Rukunin B Rukunin C Rukunin D
Katsina United Kano Pillars Wikki Tourist Enyimba
Jigawa Golden Stars Plateau United Sokoto United Rarara FC
Lobi Stars Rivers United Kwara United Elkanemi Warriors
Abia Warriors Yobe Desert Pataskum Academy DMD
Nasarawa United Kada City Kano Selected  

 

Wannan dai shine karo na uku da shugaban hukumar kwallon kafa ta Jihar Kano ke shirya wannan gasa, wadda ake gudanarwa gabanin fara kakar wasanni ta Nigeria.

Da yake zantawa da manema labarai a yayin bikin bude gasar, Shugaban hukumar kwallon kafa ta jihar Kano Shariff Rabiu Inuwa Ahlan, ya ce, duk shekara suna shirya gasar don bai wa kungiyoyin wata dama su yi shiri na musamman don tunkarar kakar wasanni da za a shiga.

Sharu Ahlan ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni musamman ma ‘yan kasuwa da su shigo su tallafa wajen bunkasa harkokin wasanni.

Harkar wasanni tafi karfin ace gwamnati ce kadai za ta yi komai, don haka akwai bukatar sauran mutane su shigo ciki musamman ma ‘yan kasuwa inji Sharu Ahlan.

A wasan farko na gasar da aka fafata kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta yi rashin nasara a hannun Plateau United da ci daya mai ban haushi.

Continue Reading

Labaran Wasanni

‘Yan wasan Nigeria na ci gaba da taka rawar gani a gasar cin kofin Zakarun Nahiyar Turai

Published

on

Yan wasan Najeriya na ci gaba da taka muhimmiyar rawa a ci gaba da fafata wasannin da gasar cin kofin zakarun nahiyar turai wato Champions league na kakar wasanni ta bana.

Daga kungiyar Slavia Prague dan wasa Peter Olayinka ya yi kokari matuka a wasan da kungiyar sa tayi rashin nasara a hannun Barcelona da ci 2 da 1.

Dan wasa Stephen Odey, ya zura Kwallo daya tilo ga kungiyar sa ta RCK Genk dake kasar Belgium wacce ta sha kashi a hannun Liverpool da ci 4 da 1.

Hakan ya biyo bayan kokarin ‘yan wasa irin su Emmanuel Dennis Bonaventure na kungiyar Club Brugge ita ma dake kasar Belgium, da dan wasa Victor Osimhen na kungiyar Lille Osc, dake kasar Faransa.

A dai gasar ta cin kofin a wasannin da aka buga da daren yau, kuma wasa na uku , shahararren dan wasan nan Lionel Messi na kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, ya bi sahun dan wasa Cristiano Ronaldo da Raul Gonzalez na kungiyar Real Madrid , wajen samun damar zura Kwallo a ragar kungiyoyi daban -daban har 33.

Haka kuma Messi ya kafa sabon tarihi na cin Kwallo a kowacce gasar na tsawon shekaru 15, wanda babu dan wasan da ya taba haka a tarihin gasar .

Dan wasan ya zura Kwallo a wasan yau da kungiyar sa ta fafata, da takwarar ta ta Salavia Prague , a rukunin F, minti 03 da fara wasan, wanda hakan ya bashi damar zura kwallayen ga kungiyoyi dai dai har 33.

kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta tsallake rijiya da baya, bayan samun taimakon na’urar hoton Video na VAR, wanda ya kashe kwallon da kungiyar Ajax ta zura mata, hakan ya bata damar zura wa Ajax din Kwallo daya tilo har gida ta hannun dan wasa Mitchy Bacshuyi.

Continue Reading

Labaran Wasanni

Shin kun san alkalin da zai busa wasan Nijeriya da Brazil?

Published

on

An bayyana sunan Jansen Foo a matsayin wanda zai yi alkalancin wasan sada zumunci da Nigeria za ta yi da kasar Brazil a ranar 12 ga watan Oktoba a babban filin wasa na kasar Singapore.

Jansen Foo dan kasar Singapore zai samu tallafin Abdul Hannan wanda zai kasance matamakin alkalin wasa na daya sai Ong Chai Lee wanda zai zamo mataimakin alkalin wasa na biyu zai kasance mataimakin alkalin wasa na hudu.

Foo wanda ya shahara wajen bayan da katin gargaji wato Yellow card ya jagoranci busa manyan wasanni guda 89.

A cikin wasanni 89 da ya jagoranta ya bada katin gargadi guda 311, sai katin kora guda 13, yayin da ya bada bugun daga kai sai mai tsaron raga guda 17.

Continue Reading

Labaran Wasanni

Tammy Abraham zai bugawa kasar Ingila wasa sabanin Nijeriya

Published

on

Biyo bayan kin bayyana sunan dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Chelsea dake kasar Ingila Tammy Abraham cikin jerin sunayen da zasu wakilci Nigeria, mai haras da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa kasar Ingila Gareth Southgate ya sanya sunan dan wasan cikin ‘yan wasan da zasu wakilci kasar ta Ingila a wasannin da zata fafata a kwanannan.

Tammy Abraham dai yana da damar ya zabi kasar kasar da zai bugawa wasa tsakanin Nijeriya da Ingila, sai da mai horas da ‘yan wasan Nigeria Gernot Rohr yace a yanzu haka Nijeriya  bata bukatar dan wasan.

Dan wasan mai shekaru 22 yanzu haka ya zurawa kungiyar kwallon kafa ta Chelsea kwallaye 7 a wasanni 7 da ya buga a gasar Primiyar kasar Ingila a kakar wasanni ta bana.

Nijeriya dai tana fama da matsalar ‘yan wasan gaba biyo bayan ritaya da Odion Ighalo ya yi.

Sai dai har yanzu Gernot Rohr bai gama gamsuwa da yadda Abraham ke taka leda ba, a don haka yake ganin yanzu Nijeriya tana da manyan ‘yan wasa wadanda suka fi Tammy Abraham iya wasa.

Continue Reading

Now Streaming

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.