Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Ahlan Cup: Yadda jadawalin gasar cin kofin ya kasan ce

Published

on

Biyo Bayan kammala shirye shiryen fara gasar share fagen tunkarar kakar wasanni mai kamawa, ta Ahlan Preseason Cup 2021, mahukuntan shirya gasar sun fitar da Jadawalin yadda gasar za ta wakana.

Kungiyar Kwallon kafa ta Gombe United da takwarar ta , ta Heartland FC ne za su bude gasar da wasan farko a ranar Talata 02 ga Nuwamba 2021, da karfe 04 na Yammaci Agogon Najeriya, a filin wasa na Sani Abacha dake unguwar Kofar Mata, a Kano.

Daga jerin Rukunin kungiyoyin da aka raba su zuwa jadawali 3 kama daga A zuwa C, sun kunshi tawagogi kamar haka…

Rukunin A

Gombe United

Heartland

El-kanemi Warriors

Kano Selected

 

Rukunin B

Wikki Tourists

Fc Yarmalight

Jigawa Golden Stars

Rarara Fc

 

 

Rukunin C

Kano Pillars

Niger Tornadoes

Doma United.

Kwamishinan wasanni na jihar Kano, Kwamred Kabiru Ado Lakwaya, ne zai kasance babban bako da zai bude tare da Kaddamar da gasar da za ta gudana tsawon mako daya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!