Labarai
Ko kun san me ya hana Ganduje nada Kwamishinoni?
Bayan da aka yi ta rade-raden da zarar ya dawo daga kasar Afrika ta Kudu zai nada kwamishinoni cikin kunshin Gwamnatin sa, kawo yanzu gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje bai sanar da ranar da zai yi wannan nadin ba.
A cikin karshen makon da ya gabata ne aka yi ta ganin kunshin sunayen tsofafi da sababin kwamishinoni, da wasu ke zargin sune kwamishinonin da Abdullahi Umar Ganduje zai nada.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewar, a cikin ‘yan kwanakin nan ne gwamnan zai sanar da sunayen kwamishinoni.
Jaridar ta rawaito cewar wata majiya mai karfi daga fadar gwamnatin Kano ta sheda mata cewar, a cikin kunshin sunayen akwai tsofafin kwamishinoni da kuma sabbin
Daga cikin kunshin sunayen akwai tsohon kwamishinan yada labarai Muhammad Garba da Murtala Sule Garo tsohon kwamishinan kananan hukumomi da Musa Iliyasu Kwankwaso tsohon kwamishinan raya karkara da kuma tsohon kwmishinan lafiya Dr, Kabiru Ibrahim Getso da dai sauran su.
Rubutu masu alaka:
Ganduje yayi Allah wadai da masu sace mutane
Gwamna Ganduje kara mayar da wasu kusoshinsa kan mukamansu
Gwamnatin Kano tayi Allah wadai da arangamar da aka samu tsakanin mafarauta a kauyen Ganduje
Amma wasu majiyoyi sun bayyana cewar meyuwa ne fadar gwamnatin Kano ta aike da kushin sunayen ne ga hukumomin tsaro don dubawa.
Kazalika wasu na ganin cewar, an sami tsaiko gabatar da sunayen sabbin kwamishinoni ne saboda jam’iyyar PDP na kalubalantar nasarar da Ganduje yayi a kotun saurarran kararrakin zabe yayin da wasu ke ganin cewar sai gwamnan yayi taza-da-tsifa wajen neman jajairtu da zasu taimaka masa.
Amma kuma tun bayan da ya samu nasarar a kotun saurarran kararrakin zabe, Gwamnan Abdullahi Umar Ganduje wasu ke saran cewar zai aike da kunshin sunayen ga majalisar dokoki ta jihar.
Sai dai da muka tuntubi sakataren yada labarai na gwamnan Abba Anwar yace shi bashi da masaniya kan wannan labarin.
Amma wakilin mu na majalisar dokoki ta jihar Kano Abdullahi Isa ya rawaito cewar, ko a zaman na majalisar na yau Litinin, bata tattauna batun gwamnan ya aike da kunshin sunayen ba.
A cewar wakilin na mu a yayin zaman majalisar na yau, majalisar ta karbi wasika daga Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje gami da wasu kudurori uku da majalisa ta 8 bata kammala aiki akan su ba.
Kudurorin dokokin sun hada da binciken harkokin kashe kudaden gwamnati da dokar bada kwangilar gwamnati ta shekarat ta 2018 da ta dokar yadda ake aiwatar da kudaden gwamnatin na shekara ta 2019, yayin da kuma dokar sabonta kwalejin nazarin aikin jinya da ungozoma ya tsallake karatu na biyu.
Yayin da dan majalisa mai wailitar Kura da Garin Mallam Hayatu Musa Dorawar Sallau ya gabatar da kudirin gyaran titin Chiromawa