Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gobara ta tashi a FCE dake Kano

Published

on

Gobarar da ta tashi a daren jiya Lahadi ta lalata ofishin adana bayanai na kwalejin ilimi ta tarrayya dake nan Kano.

Wani ganau yace gobarar ta tashi ne da misalin karfe tara 9 da rabi na daren jiya Lahadi.

Rahotanni sun bayyana cewar ‘yan kwana-kwana da jami’an tsaro  da wasu daga cikin dalibai sun yi kokarin kashe gobarar wanda ya hana bazuwar ta zuwa sauran ofisoshin.

Haka zalika wadanda al’amarin ya afku akan idanun su, sun ce babu wanda ya samu rauni a yayin da gobarar ta tashi.

Shugaban kwalejin Dr, Sadi Suraj ya je wurin da sauran malaman makarantar, yayin da suka yi amfani da abun kashe gobara don hana ta bazuwa zuwa sassan kwalejin.

Duk kokarin mu na tuntubar jami’in yada labarai na kwalejin Auwal Mudi Yakasai ya ci tura bayan da wayar sa taki shiga.

Sai dai jami’in yada labarai na hukumar kashe gobara ta jihar Kano Sa’idu Muhammad Ibrahim yace sun samu kira ne daga wani bawan Allah yayin da jami’an su, suka gaggauta zuwa wurin.

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!