Connect with us

Manyan Labarai

Shin rigimar Ganduje da Kwankwaso tazo karshe?

Published

on

A ranar 21 ga watan Oktoban da muke ciki ne tsohon Gwamnan jahar Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya cika shekaru 63 a Duniya.

Bikin ranar cikar tsohon Sanatan na Kano ta tsakiya shekara 63 ya kawo abubuwa da dama da suka hada da yin abubuwa da suka shafi bikin  haihuwar  ta sa.

Lokacin da ake bikin na tsohon Gwamna Inijiya Rabiu Musa Kwankwaso sai ga shi wani abun mamaki ya bayyana inda tsohon abokin sa da suka kusa shekaru ashirin suna siyasa tare, wato Gwamnan Kano mai ci a yanzu, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana a shafin wata shararriyar jarida yana taya tsohon mai gidan nasa a siyasa murnar cikar sa shekaru 63 a Duniya.

Wannan sako na taya tsohon Gwamnan na Kano kuma tsohon abokin siyasar Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje a siyasance  murna ranar haihuwa ya bawa al’umma da dama mamaki, sakamakon rashin ga miciji da manyan ‘’yan siyasar biyu na jahar Kano ke yi tun sanda dagantakar ta su tayi tsamari.

Shi dai tsohon Gwamnan jahar Kano inijinya Rabiu Musa Kwankwaso ne a watan Nuwambar shekarar 2014 ranar alhamis 27 ga watan na Nuwamba a taro da ya gudana a dakin taro na Afrika House ,ya nuna tsohon mataimakin sa  a matsayin wanda zai yi takara shi kadai daga tsagin tsohuwar darikar Gwanma Abdullahi Umar Ganduje wato darikar ta Kwankwasiyya a jamiyyar APC  ,dan tunkarar babban zaben Najeriya da ake sa ran gudanarwa a shekarar 2015.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yayi takarar neman tsayawa  Gwamna a zaben fitar da gwani da jamiyyar APC ta gudanar a ranar 4 ga watan Disamba na shekarar 2014.

Daga cikin wanda suka nemi takarar Gwamna da Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje akwai Sakataran gwamnatin jahar Kano na yanzu ,Alhaji Usman Alhaji da kuma tsohon dan majalisar wakilai kuma wanda ya taba bawa shugaban kasa Muhammadu   Buhari shawara akan harkokin majalisa wato Honorable Abdurrahman Kawu Sumaila .

Dab ,da zaa fara zaben fitar da gwanin wasu daga cikin ‘’yan takarar suka janye, da suka hada da shi sakataran gwamnatin na jahar Kano Alhaji Usman Alhaji tare da Abdurrahman Kawu Sumaila.

Da aka cigaba da kokarin fitar da gwani tsohon kantoman mulkin soja na Jahar Kaduna mai ritaya Birgediya Janar Lawal Jaafaru Isa ne ya tsaya takara da Gwamnan na Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje wanda Gwamna Ganduje yayi nasara a fitar da gwani da jamiyyar ta APC din tayi ,

Bayan shiga zaben shekarar 2015 Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yayi nasara.

An rantsar da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 2015 bayan tsohon Gwamna Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya mika masa mulki.

Kafin sabuwar shekarar 2016 ne ake ta rade radin akwai rigima ta siyasa tsakanin tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamna mai ci Dr Abdullahi Umar Ganduje ,

Kwatsam sai lokacin da mahaifiyar Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ta rasu, sakamakon zuwa gaisuwa da Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso yayi ,Gwamnatin ta jahar Kano ta zarge shi da rashin da’a ,har jamiyyar APC  tace zata ladabtar da Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso akan diban wadanda ake zargi ‘’yandaba ne zuwa gaisuwar  mahaifiyar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Tun daga wannan lokaci ne aka fada rikicin siyasa tsakanin Gwamna Abdulahi Umar Ganduje da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ta cigaba da ruruwa har dab da zaben shekarar bana.

A shekarar 2018 ce dai tsohon Gwamnan Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya koma tsohuwar jamiyyar sa ta PDP, inda daga nan ne  rikicin siyasar ta jahar Kano bata tsagaita ba ,har bayan zaben na shekarar 2019.

Amma sai ga shi kwatsam a ranar 21 ga wata Gwamnan na Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya taya tsohon Gwamnan na Kano kuma tsohon shugaban sa, a siyasa injiniya Rabiu Musa Kwankwaso murnar cika shekaru   63 a Duniya.

Continue Reading

Labarai

WAEC ta fitar da sakamakon jarrabawar bana

Published

on

Hukumar shirya jarrabawar kammala sakandare ta Afirka ta yamma WAEC ta fitar da sakamakon jarrabawar dalibai dubu casa’in da daya da dari biyu da ashirin da biyar na wadanda suka rubuta jarrabawar masu zaman kansu na  bana a Najeriya.

Babban jami’in hukumar a Najeriya Mr Olu Adenipekun ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar yau, inda ya ce akalla dalibai dubu casa’in da bakwai da tamanin ne suka yi rajistar jarrabawar inda kuma dubu casa’in da hudu da da dari takwas da tamanin da hudu ne suka zauna jarrabawar a kasar nan.

Ya kuma kara da cewa akwai sakamakon jarrabawar dalibai dubu uku da dari shida da hamsin da tara da har yanzu ba a fitar da sakamakonsu ba sakamakon ci gaba da duba jarrabawar da ake yi.

Jami’ar Bayero ta kama dalibai shida da zargin magudin jarrabawa.

BUK ta kori dalibai 63 saboda satar jarrabawa

Hukumar JAMB ta sanar da ranar sake rubuta jarrabawar ga dalibai fiye 12,000

Haka zalika Adenipekun ya bayyana cewa a Najeriya dalibai dubu arba’in da bakwai da dari biyu da talatin da bakwai ne maza yayin da mata suka kasance guda dubu raba’in da bakwai da dari shida da arba’in da bakwai suka zauna rubuta jarrabawar a bana.

Continue Reading

Labarai

Ganduje- mun kammala biyan diyyar aikin gadar Dangi

Published

on

Gwamnatin jihar Kano tace ta kammala biyan dukkannin diyyar gidaje da shaguna daya dakatar da aikin Gadar Sama da kasa dake Titin Dangi dake nan Kano.

Kwamishin ayyuka da raya kasa na jihar Kano Alhaji Mu’azu  Magaji ne ya bayyana hakan yau lokacin fara rushe gidajen da aka kammala biyan diyyar cigaba da gudanar da aikin gadar kasa da dama na Dangi.

Agefe gudu kuma masu gunadanar da sana’oin su a guraran na cigaba da korafi kan yadda aka basu wa’adin kwana guda tak su kwashe kayayyakin su daga wajen don cigaba da aikin.

Gwamnatin tarayya bata gudanar da ayyukan tituna yadda ya kamata ba

Gwamnatin Kano zata cigaba da yada da’awa

Gwamnatin tarayya ta bada hutun Maulidi

A cewar kwamishinan Alhaji Mu’azu Magaji gwamnan kano Abdullahi Umar Ganduje na bukatar ganin aikin gadar ya kammala cikin kankanin lokaci.

Wakilin mu Abdulkareem Muhammad Abdulkareem Tukuntawa ya rawaito cewa, an dai rushe wasu daga cikin gedajen da aikin ya ratsu ta cikin su.

Continue Reading

Labarai

Ganduje- mun kammala biyan diyyar aikin gadar Dangi

Published

on

Gwamnatin jihar Kano tace ta kammala biyan dukkannin diyyar gidaje da shaguna daya dakatar da aikin Gadar Sama da kasa dake Titin Dangi dake nan Kano.

Kwamishin ayyuka da raya kasa na jihar Kano Alhaji Mu’azu  Magaji ne ya bayyana hakan yau lokacin fara rushe gidajen da aka kammala biyan diyyar cigaba da gudanar da aikin gadar kasa da dama na Dangi.

Agefe gudu kuma masu gunadanar da sana’oin su a guraran na cigaba da korafi kan yadda aka basu wa’adin kwana guda tak su kwashe kayayyakin su daga wajen don cigaba da aikin.

Gwamnatin tarayya bata gudanar da ayyukan tituna yadda ya kamata ba

Gwamnatin Kano zata cigaba da yada da’awa

Gwamnatin tarayya ta bada hutun Maulidi

A cewar kwamishinan Alhaji Mu’azu Magaji gwamnan kano Abdullahi Umar Ganduje na bukatar ganin aikin gadar ya kammala cikin kankanin lokaci.

Wakilin mu Abdulkareem Muhammad Abdulkareem Tukuntawa ya rawaito cewa, an dai rushe wasu daga cikin gedajen da aikin ya ratsu ta cikin su.

Continue Reading

Now Streaming

Freedom Radio Kano
Please wait 20 seconds Or Click on to Play.…

Now Streaming

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.