Labarai
An mika yaran da aka sace ga iyayen su a Gombe
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Anambra ta ce ta mika yara biyu da aka sace su a jihar da iyalan su, bayan da aka tabbatar da cewa iyayen su ‘yan asalin jihar Gombe ne.
Rahotannin sun bayyana cewar, rundunar ‘yan sanda ta jihar Anambra ta sanar da cewa ta gano wasu yara biyu da ake zargin an sace su kuma an saida su a jihar ta Anambra.
Wannan dai shi ne karo na cikin wata guda da jami’an ‘yan sada suka gano makamanci irin wadannan nan aika-aika a jihar ta Anambra.
Tun da fari dai a farkon wannan watan na Okotoba dake neman karewa rundunar ‘yan sandan Kano ta gano mutum tara ‘yan asalin jihar nan da aka sace su kuma aka saida su a can jihar Anambra.
‘Yan sanda sun kara ceto yara biyu da aka sace a Anambra
Iyayen yaran da aka sace sun bukaci taimakon al’umma
An yiwa daya daga yaran Kano da aka sace fyade
Akan haka ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin da gudanar da bincike akan yadda aka sace yaran da kuma saida su a can jihar ta Anambra.
Kazalika gwamnatin Kano ta kafa kwamitin bincike kan yaran da aka sace su Arba’in da Bagwai bayan da aka saida su a jihar Anambra.
A dai ranar Juma’ar da t agabata ne kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Anambra Haruna Mohammed ya sanr da cewar jami’an rundunar suka kama wasu mata uku da ake zargin sato wasu yara biyu sai dai ba’a san inda Iyayen su, suke ba.