Labarai
An zargi DPO da hannu wajen kisan kai
Lauyoyin Kare hakin dan Adam na cigaba da Bincike akan matashin nan da “yan sandan madobi suka doka har ta kai ga ya dukan yayi sanadiyyar mutuwar sa.
An gano cewa baturen ‘’yansanda na Madobi na da hannu wajen dukan matashin inda a wani bangare “yan sandan masu bincike sun ce basu kama baturen yansandan da laifin da ake zargin sa dashi ba .
Lauya dan gwagwarmaya Barrister Abba Hikima Fagge, yace zasu cigaba da bibiya domin gane gaskiyar al’amarin da yadda bincike yake tafiya, sannan kuma ya kalubalanci hukumar “yan sanda akan kyale baturen ‘’yansandan da ake zargi da cigaba da harkokin sa ba tare da an tsare shi ba duk da zargin da ake masa da sak hannu wajen dukan wannan bawan Allah da takai har ya rasu.
A nata bangarin rundunar “yan sandan Jihar Kano ta hanyar mai magana da yawunta, D.S.P Abdul Haruna Kiyawa yace har izuwa yanzu binciken su bai nuna cewa wannan baturen ‘’yansanda na Madobi na da hannu a dukan wannan bawan Allah amman suna cigaba da bincike kuma zasu yi Adalci.
Yadda matashi ya rasa ransa a hannun ‘yan sanda
‘Yan sanda sun cafke sojoji kan KAROTA
Zamu dauki mummunan mataki kan Zakin da ya kubuce –‘Yan sanda
A wani labarin kuma “yansandan Shiyya ta daya dake Kano sun kama wasu “yan sanda da suke amfani da kayan kaki suke karbar kudi a hannun mutane a Unuguwar Sabon Gari .
Kakakin rundunar S.P Sambo Sokoto yace suna cigaba da bincike akan wadannan mutane da aka kama kuma iya binciken da sukayi ya tabbatar da cewa babu wani Dansanda a cikin wadannan mutanen.