Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kotun daukaka kara ta sanya ranar shari’ar Ganduje da Abba

Published

on

Kotun daukaka kara da ke Kaduna ta ayyana ranar litinin na makon gobe sha daya ga watan Nuwamba a matsayin ranar da za ta fara sauraran daukaka kara da dan takarar gwamnan jihar Kano karkashin jam’iyyar PDP Abba Kabir Yusuf ya shigar gabanta, yana kalubalantar nasaran gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje.

A yau Alhamis ne dai kotun ta sanar da jam’iyyun PDP da APC kan shirinta na fara sauraran daukaka kara da Engineer Abba Kabir Yusuf ya shigar gabanta.

Rahotanni sun ce kotun tana da wa’adin nan da ranar talatin ga wannan wata da muke ciki domin yanke hukunci kan shari’ar.

Sashe na dari biyu da tamanin da biyar na Kundin tsarin mulkin kasar nan na alif da dari tara da casa’in da tara, wanda aka yi wa gyaran fuska, ya bayyana cewa, an kayyade wa kotun daukaka kara, wa’adin kwanaki sittin da ta yanke hukunci, farawa daga ranar da kotun sauraran korafin zabukan gwamnoni ta yanke hukunci.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!