Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kano9: Karanta cikakken labarin yaran Kano da aka sace

Published

on

A dai kwanakin baya ne rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta sake gano  wani Yaro tare da ceto shi daga jihar Anambra wanda wasu suka sace shi  mai suna Salisu.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano Ahmad Iliyasu kuma mataimakin babban sufeton ‘yan sanda na jihar Kano ya bayyana hakan taron manema labarai a jiya Alhamis.

Hakazalika Kwamishina Ahmad Iliyasu ya ce a halin yanzu ba yara tara ba ne yara goma ake magana.

Ahmad Iliyasu ya ce a jiya yaron Salisu suna kan hanyar su ta zuwa a nan Kano amma kuma ana kyautata zaton cewar za su iso yau da safe.

Idan za’a iya tunawa a kwanakin baya ne rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta sanar da cewar ta ceto yara tara 9 ‘yan asalin jihar Kano da aka sace su aka kuma saida su a can jihar Anambra.

Yaran Kano 9: Ganduje ya kafa kwamitin bincike na musamman:

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kafa wani kwamitin bincike, don bin diddigin kan kwato hakkokin yaran nan 9 da aka ceto daga hannun masu satar mutane da suka sayar da su a Jihar Anambra.

Daga cikin aikin da kwmaitin zai yi shi ne, bibiyar duk mutanen da aka sace a nan Kano tun daga shekarar 2010 zuwa yanzu ta hanyar jin ra’ayoyin shaidu ta baka ko a rubuce, domin samun makama a kan binciken, tare da gano dalilan batan na su.

Sakataren yada labaran gwamnan Abba Anwar ne bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar yau Juma’a, inda ya bayyana cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana sunan Justice Wada Umar Rano a matsayin wanda zai jagoranci kwamitin.

Sanarwar ta kara da cewa, ranar alhamis mai zuwa 31 ga watan Oktoban nan da mu ke ciki gwamnan zai kaddamar da kwamaitin.

Tun a cikin shekarar 2015 ne dai al’ummar Unguwannin Hotoro da Kawo da Walalambe da Walawai da kuma Tinshama dukkansu a karamar hukumar Nassarawa a Kano, suka koka da cewa an sace mu su yara akalla 47.

A baya-bayan nan ne dai rundunar yan sandan Jihar Kano ta bankado gungun masu satar yaran suna sayar da su Jihar Anambra tare da sauya mu su addini zuwa kiristoci, inda ta ceto yara 9 daga hannunsu.

Ganduje ya hana iyayen yara Magana da yan jarida:

Gwamna Abdullahi Ganduje ya ja hankalin iyayen da aka ceto ‘yayansu daga Onitsa jihar Anambra da su yi hankali da yan jarida kungiyoyi masu zaman kansu.

Gwmamna Ganduje ya bayyana haka ne ayayin da rundunar yan sanda jihar Kano ke mika wadannan yara hannun gwamnati a ranar litinin da ta gabata.

Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwar mai dauke da sa hannun daraktan yada labarai na gidan gwamnati Aminu Yassar ya fitar kamar yadda jaridar Kano Focus ta rawaito.

Gwamna Ganduje ya ja hankalin iyayen yara da yaran da su kauracewa zantawa da yan jarida da kungiyoyi masu zaman kansu, gudun kada wasu yan jaridun ko kungiyoyi masu zaman kansu samun damar amfani da su domin cimma wata manufa ta su.

Yana mai jaddada cewa hukumomin tsaro na gudanar da bincikensu gudun kada hakan ya kawo cikas ga bincikensu.

An yiwa daya daga yaran Kano da aka sace fyade:

Daya daga cikin yara tara da aka ceto a garin Onitsa dake jihar Anambra, ta fuskanci cin zarafi na fyade a hannun wanda suka sace ta, kamar yadda cibiyar da ke lura da wadanda suka fuskanci matsala ta fyade ta bayyana.

Manajan cibiyar Nasiru Garko ne ya bayyanawa jaridar Kano Focus cewar, bayan duba daya daga cikin yaran yar shekara 10 domin tabbatar da ba ta dauke da wasu cutuka da ake samu ta hanyar cin zarafi.

Malam Garko wanda likita ne ya tabbatar da faruwar hakan.

Ya ce yarinya ta bayyana cewar an aikata fyade da ita sau da dama daga hannun wanda ya sace ta.

An dai kafa wannan cibiyar ne a karkashin kulawar asibitin kwararru na Murtala Muhammad dake nan Kano.

Kawun yarinyar wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce babban burinsu shine a bi musu hakkinsu dangane da garkuwa da akayi da yarsu.

Ya na mai cewa zasu tattaua don ganin an shigar da kara akan cin zarafi da aikata fyade da aka yi akan ‘yar ta su.

 Yaran Kano: Majalisar dokokin Kano zata dauki mataki:

Majalisar dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin jiha da ta gaggauta daukan mataki tare da bibiyar sauran yara ‘yan asalin jihar Kano da har yanzu suke hannun wadanda suka sacesu a ka boyesu a jihar Anambra.

Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin gaggawa da shugaban masu rinjaye na majalisar Abdul Labaran Madari ya gabatar yayin zaman majalisar na yau.

Majalisar ta kuma bukaci kungiyar jamaatu Nasril Islam da ta fito fili tayi Allawadai da sace yara a kano ana sauya musu addini.

Haka zalika majalisar ta yabawa rundunar ‘yansandan jihar kano sakamakon kokarin da ta ce tayi wajen nasaran ceto yaran.

Bayan da gabatar da kudirin Abdul Labaran Madari ya kuma ce kamata yayi gwamnati Kano da ta gaggauta kafa kwamtin da zai bibiyi yadda za’a dawo da yaran a kuma sada su da iyalan su.

Daga bisani majalisar dokokin ta Kano ta amince da kudirin.

 

Satar yaran Kano da munafurcin kafafan yada labarai:

A ranar jumaar da ta gabata ce rundunar yansanda ta jahar Kano tayi holen wasu mutane da suka sace kananan yara ‘’yan asalin jahar Kano zuwa jahar Anambra tare da sayar da su a garin Onitsha.

Rahotanni sun nuna cewa ba’a nan kawai ta tsaya ba, bayan satar yaran an canja musu addini daga na musulunci zuwa kiristanci, tare da  mayar da su bayi.

Tun shekarar 2014 ne dai al’ummun wasu yankuna dake nan Kano da suka hada da unguwar Hotoro da Yankaba da Sauna da Kawaji da Dakata anan Kano suka rika korafin cewa ana sace musu yara kanana  .

Satar yara kananan ya tayar wa da iyaye da dama hankali inda wasu daga cikin iyayan suka shiga bakin cikin rabuwa da ‘yayan nasu sakamakon sace su da aka yi a tsawon shekara biyar.

An dade ana tafka mahawara tsakanin al’umma daban daban anan Kano a game da dalilin da yasa ake satar yara a Kanana kuma  ba tare da an gansu ba.

Ko a kwanakin baya sai da aka cafke wani dan kabilar Igbo a tashar motar sabongari da ake kira da a turance luxurious Bus station ya sace wani yaro a yankin unguwar Yankaba zai yi kudancin Najeriya da shi domin aikata ita wannan mummunar adawa ta sayar da yaran Kano.

Cafke wannan dan kabila ta Igbo shi ya saka rundunar ‘’Yanasandan jahar Kano karkashin tsarin nan na operation puff Adder suka shiga bibiyar wannan lamari har aka zo ga matakin da ake ciki na cafke masu satar yaran Kano da sayar da su da kuma canja musu Addini a yankin na kudu maso gabashin Najeriya.

Amma abun tambaya anan shi ne ,lokacin da labaran sace yaran suka yadu a kafafan yada labarai irin su jaridun Daily Nigeria , wasu daga cikin jaridun kasar nan basu mayar da hankali akan labaran da ya fito daga jahar ta Kano ba ,na sace yaran da mayar da su wani addini da ba nasu ba.

A lokacin da jaridun kudu suke bawa labarai da basu taka kara sun karya muhimmanci ba, da sauran al’amura na yau da kullum , sai ga shi labarin na yaran Kano bai zama labara mai muhimmanci ga jaridun na kudancin kasar nan ba.

A farkon shekarar 2016 ne dai wani dan asalin jahar Kano mai suna Yunusa Yellow aka zarge shi da tahowa da wata yarinya daga jahar Bayelsa mai suna Ese Oruru da aurar da ita har da zargin canja mata addini duk da zargin da aka yi na cewa ya aureta.

A wannan lokaci jaridun kudancin kasar nan sun yi nisa  wajen ganin an kwatowa wannan yarinya ‘’yar asalin jahar Bayelsa Ese Oruru hakkin ta na ganin cewa ta samu yanci daga hannun matashi dan asalin karamar hukumar Kura.

Yunusa Yellow ta kai ga an gabatar da shi a babbar kotun tarayya dake  Yenagoa babban birnin jahar Bayelsa.

Bayan nan jaridu irin su jaridar Sun, da sauran su, sun bibiyi labarin na Ese Oruru har zuwa garin na su domin bin bahasi akan abun da ya faru tsakanin Ese Oruru da Yunusa Yellow dan asalin karamar hukumar Kura.

Kungiyoyin Musulmi da dama da sauran kungiyoyi da na malamai sun yi shiru, banda kungiyar Muslims Right Concern wato MURIC da suka fitar da bayanai na tir da abunda ya faru na satar yaran na Jahar Kano.

Ko ina kungiyar hana fataucin yara da ta NAPTIP take, na gano matsalar da ake ciki a jahar Kano na sace yaran garin.

Ya kamata ace tuntuni Gwamnatin jahar Kano ta binciki abubuwan dake faruwa a wannan tashar ta  Sabongari da ake amfani da ita, na diban yaran Kano domin mayar da su wani addini da ba nasu ba, kuma a matsayin su na kananan yara da aka keta musu hakki.

Yaran Jahar Kano: Me yasa Buhari bai magantu da wuri ba?

Tun lokacin da bayanai suka fita a kafafan sadarwa da kafofin yada labaran kasar nan na yanar gizo na sace yaran jahar Kano, kungiyoyin addini suka fara magantuwa akan sace yaran na Jahar Kano zuwa jahar Anambra domin mai da su kirista.

Duk da maganganun da aka rika yi na kiraye kirayen alúmma su yi magana domin kwato hakkin yaran ‘’yan asalin jahar Kano, wanda alúmmar jahar Kanon suka damu da rashin yin maganar tasa shi ne shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ita dai fadar shugaban ta Najeriya ba ta fitar da matsayar ta akan sace yaran Kano din guda tara ba ,har sai da aka kai kwanaki takwas da fallasar wannan lamari .

Jamaa da dama dai suna ganin jahar Kano itace cibiyar siyasar shugaba Muhammadu Buhari, inda suke ta dakon suga ya magantu game da sace yaran na Jahar Kano, amma hakan ta faskara har sai bayan kwanaki takwas.

Kungiyoyi irin su Muslim rights concern wacce Farfesa Ishaq akintola ke shugabanta itace kungiyar Musulmin Najeriya ta farko da ta fara fitar da matsayinta ,sannan tayi tir da dabi’’ar wasu daga cikin kabilar Igbo na kasar nan da suka sace yaran Kano tare da sayar da su.

Sai daga baya kungiyoyi suka rika biyowa irin su kungiyar kabilar Igbo ta jahar Kano inda ta nesanta kanta daga wadanda suka sace yaran na jahar Kano .

Ita ma kungiyar kiristoci ta Najeriya reshen jahar Kano ,tayi tir da lamarin inda tace wadanda suka sace yaran na Jahar Kano ba kiristoci bane kuma basu da alaka da tanade tanaden addinin kirista.

Matsin lambar da fadar shugaban kasar ta fuskanta a kafafan sada zumuntar ya jawo cecekuce tsakanin wasu daga cikin magoya bayan shugaba Muhammadu Buhari da sauran alúmma.

Shi dai shugaban kasa Muhammadu Buhari mutum ne mai, farin jini a jahar ta Kano tun daga ranar da ya shiga siyasa ya yanki katain tsohuwar jamiyyar APP a mazabar sa ta Daura ranar 25 ga watan Afrilun shekarar 2002.

Duk zabukan da shugaba Muhammadu Buhari ya rika tsayawa duk da zargin tafka magudi da aka ce anyi a zabukan kasar nan, shugaban bai taba faduwa zabe a jahar Kano ba.

Wannan dalili ne ya sa masana suke ganin cewa a tarihin siyasar shugaba  Buharin, bashi da garin da ya wuce jahar Kano da zai kira ta a matsayin cibiyar siyasa.

Ko jamiyyar CPC da shugaban yayi mata takara a shekarar 2011 , sai da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kayar da takwaransa a takarar shugaban kasa kuma Gwamnan jahar Kano mai ci na wancan lokaci, wato Malam Ibrahim shekarau na jamíyyar ANPP.

Tun dai sanda shugaban kasar ya dare karagar mulkin Najeriya a shekarar 2015 , alúmmar ta jahar Kano suke ganin kamar shugaban yana ko in kula da lamarin su, duk da cewa itace jahar da tafi rabauta da mukaman Gwamnatin tarayya masu gwabi gwabi daga yankin arewacin kasar nan.

Kwanaki takwas da fadar shugaba Buhari ta dauka bata ce komai ba akan sace yaran na jahar Kano ya matukar tunzura wasu daga cikin alúmma har suke ganin ko shin shugaban ya damu dasu.

Ko a zaben shekarar bana al ‘ummar ta jahar Kano basu kwayewa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya ba, inda suka sake afka masa kuriu fiye da miliyan daya kamar yadda suka saba ,ya sake lashe zaben shugaban kasa a karo na biyu da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairun shekarar ta 2019.

Shin ko laifin waya wajen jan kafa na fitar da bayanan shugaban kasa musamman ma idan ya shafi alúmmar jahar Kano ?

Kano yara 9: taron wasu mata sun bukaci sa hannun majalisar Kano

Wasu gungun mata su ashiri a yau suka hadu suka hallarci majalisar jihar Kano domin samun goyon bayan majalisar dangane batun sace tare da gano yara tara da aka yi ‘yan jihar Kano.

Gungun matar karkashin hadakar malamai da kungiyoyi masu zaman kansu, sun bukaci majalisar da ta samar da wani kwamiti da zai bincike al’amarin

Shugabar tawagar Amira Halima Shitu-Abdulwahab ta ce makasudin kiran nasu domin kawar da duk wani tsaiko da ke hana hukunta doka akan masu irin wannan laifi tare da tabbatar da an hukunta su.

Ta ja hankalin majalisar da su karfafa wajen sabunta dokar da ke batun kan sace yara ko sabunta dokokin domin kawo karshen wannan matsala.

Hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da laifin sace yara da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bukata abu ne mai kyau da ya kuma dace.

Matan sun kara jan hankalin majalisar da bibiyi hukumar da ke lura da al’amarin tare da tabbatar da gwamnatin Kano ta bi dukkanin hanyoyin da ya dace.

Sun kuma bukaci gwamnati da ta taimakwa wajen baiwa hukumomin tsaro dukkanin kulawar da ta dace domin gano ragowar yaran da aka sace kuma har yanzu ba’a kai ga ganinsu ba.

Tare da bukar majalisar ta samar da dokar da zai bada damar rufe dukkanin gidajen da aka kama da sace yara ko masu garkuwa da mutane.

Da yake Magana shugaba majalisar Abdulazeez Garba-Gafasa, yay aba da yunkurin matan tare da shan alwashin magance matsalar .

Garba-Gafasa  ya ce majalisar zata samar da hanyar da za’a magance matsalolin garkuwa da sace yara a fadin jihar Kano.

Hukuncin Kisa ne ga masu Satar mutane-Ganduje:

Gwamnatin Kano ta baiwa kowanne guda daga cikin yaran da aka ceto su bayan da aka sace su a kai su jihar  Anambara a baya-bayan nan su tara Naira miliyan guda.

Gwamnan jihar Kano Dr, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan a jiya yayin da yake kaddamar da kwamitin mutum goma sha shida 16 da za su gudanar da bincike kan yadda aka sace yara fiye da Arba’in  40 aka saida su a can jihar Anambra tun daga shekara ta 2010 zuwa ta 2019 da muke ciki.

Da yake jawabi bayan kaddamar da  gwamnatin, gwamnan na Kano Abdullahi Umar Ganduje ya baiwa kwmaitin kwanaki Talatin da ya kamala binciken sa ya mikawa gwamnati rahoto karkashin jagorancin mai shari’a Wada Umar Rano mai ritaya.

Haka zalika gwamnan na Kano ya yi alkwarin daukar nauyin yaran Tara  da su yi karatu tun daga makarantar  Firamare zuwa matakin Jami’a, ya kuma sake nanata cewar  gwamnatin sa zata sake yi wa dokar sake mutane d ayin garkuwa da su garanbawul don zartar da hukuncin kisa ga wanda ya sace mutane.nan bada jimawa ba.
Wakilin mu na fadar gwamnati Aminu Halilu Tudunwada,ya rawaito cewar an rantsar da kwamitin mutum goma sha sheda 16 da suka hada da rundunar sojan kasar nan da ta shige da fice da jagororin alummar kabilar Igbo da malaman addinai da kungiyoyin kishin alumma da masu rike masarautun gargajiya da kuma manyan jami’an gwamnati.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!