Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Shin ina makomar matsalar gurbatar muhalli a Jihar Kano

Published

on

Mazauna Unguwar rukunnin kamfanoni na Sharada da Challawa da Bompai  da ke jihar Kano na fama da matsanacin yanayi na gurbatar muhalli da ya danganci dagwalon masana’antu da gurbatar iska musammam ma a lokutan yanayi na zafi.

Shekaru da dama gidan rediyo Freedom ke rahoto dangane da irin matsanacin hali da wadannan alumma ke fuskanta har ta kai da an kai wasu daga cikin wadannan kamfanoni kotu, amma har kawo yanzu hakarsu bata cimma ruwa ba.

Labarin gwagwarmayar wadannan yankunan dai ya shafe shekaru da dama ana yi inda suka kai korafai-korafai a hukumomin da ya kamata, a wannan yunkuri ne aka yi nasarar kaddamar da wata hukuma da ke lura da gurbatar yanayi na Challawa da kuma daya da aka samar a rukunin kamfanoni na Bompai a jihar ta Kano.

Ana wannan yunkuri ne dai wani kamfani daga kasar Jamus a ‘yan shekarun da suka gabata suka nuna damuwarsu da son zuba hannun jari domin kawo karshen wannan matsala ta gurbatar yanayi da wadannan yankuna ke fama da shi, wannan kudiri nasu na neman zaman labarin kanzon kurege.

Sakataren gwamnatin tarayya,babban sakataren hukumar asusun ayyukan muhalli- sabon rikici

A rahoton wani bincike ya nuna cewar sakataren gwamnatin tarayya , Boss Mustapha ya amince da wannan kudiri na kawo karshen wannan matsala ta dagwalon masana’antu, inda ya sa hannun gudanar da wannan aiki akan  fiye da naira miliyan 417,990,976.30 inda aka baiwa wani kamfani mai suna Messrs Alps Global link limited.

Sakataren gwamnatin ,a wasu takardu da jaridar Newsdairyonline ta binciko ya nuna amincewar gwamnati ta hanyar fitar da kudade ga wani kamfanin na Messrs. Westgold engineering da development consultant limited,.

Haka kuma wannan bukata tuni aka sake zantawa da shi sakataren gwamnatin inda babban sakatare a hukumar lura da kudaden tallafin ayyukan muhalli wato Ecological fund EFO.

Dr Habiba Lawal a wata takarda da tasa  hannu na ranar 1 ga watan Nuwamban wannan shekara mai dauke da lamba Reference Number EF/PROC/PC/187/VOL.1/149 ya bayyana cewa an amince da bukatar ta na ranar 5 ga watan Nuwamban wannan shekara ,a lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya kai ziyara birnin London.

Ko da yake masu ruwa da tsaki na jihar Kano sun bayyanawa jaridar Newsdairyonline cewar kamfanin da zai karbi wannan kudade na Apls Global Links Limited  ba shi ne ya cancanci karbar wannan kwangila ba, kuma ba shi ne ya fara gudanar da bincike ba wuraren wadannan unguwanni da ke fama da dagwalon masa’antu wanda aka yi da hadin gwiwar gwamnatin jihar Kano tun farkon shekara ta 2010.

Takardun sun bayyana cewar wani kamfani dake zamansa a kasar Jamus , wato German Company Deutsch Africa ,ne suka fara wannan bibiyar yadda aikin zai kasance wanda tuni ma suka ziyara  gwamnatin jihar Kano domin aikin.

Tuni dai ridici ya barke  , a lokacin da asusun na ecological fund na kokarin watsi da aiki da kamfanin na Jumas duk da kwarewarsu da nuna son gudanar da aikin.

Shin an yaudari shugaba Buhari ne?

Bincike ya nuna cewar takardu da suka danganci lamarin ,nuni da  cewar sakataren gwamnatin tarayya bai sanar da shugaba Buhari tare da bashi damar zabar kamfanin da ya dace ba ,hasali ma, an mika masa takardun ne domin ya sanya hannu dangane da ayyukan da suka shafi muhalli na jihar Kano.

Bincike ya nuna cewar ko a cikin takardar, ba’a nunawa shugaba Buhari cewar akwai wani kamfani daga kasar Jamus da zai zuba hannun jari na bibiyar al’amari tun shekara ta 2010, wanda tuni suka zanta da masu ruwa da tsaki da suka shafi matsala ta dagwalon masana’antu.

Kwatsam sai ji suka yi am baiwa wani kamfani da basu da masaniya da al’amari.

A shekara ta 2016 ne kamfanin Deutsch Afrika dai sun rubutawa babban sakataren gwamnatin tarayya wasika dangane da irin tsare-tsaren da suka fitar n a yadda zasu samar da wata hanya guda daya da ruwan dagwalon masana’antu zai dinga bi a fadin jihar Kano.

Indai masu sauraro basu  manta ba gidan Freedom radio ta sha kawo rahotanni na yadda alummar Sabuwar gandu,da Sharada da ma Bompai har da ”yan garin Wudil wanda wannan ruwa na dagwalon masana’antu ke shiga kogin Wudil yake kashe kifaye da ke ciki.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!