Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Yaran da aka sace sun kaiwa Ganduje ziyara

Published

on

Rundunar yan sandan jihar Kano ta mika yara takwas daga cikin tara da aka ceto daga hannun masu satar yara, aka kuma sayar da su a jihar Anambra ga gwamnatin Kano.

 

Ko da yake yaro daya daga cikinsu dai a yanzu haka bashi da lafiya wanda yake karbar magani a asibiti.

 

Da yake karbar yaran da aka kubutar a gidan gwamnati, gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje wanda sakataren gwamnati Alhaji Usman Alhaji ya wakilce shi ya bayyana jin dadin sa na ceton yaran, tare da jadadda cewar rundunar ‘yan sandan jihar Kano tayi abin a zo a gani.

 

Ya kara da cewa gwamnatin Kano tana tattaunawa da hukumomin tsaro tun da abin ya faru, tare da tabbatar da cewar faruwa al’amarin bai haifar da abin da zai ta da zaune tsaye ba.

 

Ya kuma sha alwashin cewar gwamnati zata jajirce wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummarta, yana mai jan hankali iyaye da su dinga sanya idanu kan ‘yayansu tare da lura da dukkanin al’amuran da su ke yi mussamam ma ta hanyar amfani da wayoyin salula.

Rundunar ‘yan sanda ta Kano zata fadada bincike a Anambra

 

Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban daraktan yada labarai na gidan gwanati Ameen Yassar.

 

Gwamnan Kano yana mai jan hankalin iyayen da aka ceto yaransu da su san cewar a yanzu haka ana bincike kan lamarin a don haka su lura da dukkanin abubuwan da suke fada ko aikatawa gudun kada hakan ya kawo cikas ga aikin da hukumomin tsaro ke aikatawa a yanzu.

 

 

Ya ce gwamnatin Kano zata fito da wani shiri na mussamam ga yaran da aka ceto, a yayin da yake zantawa da yaran da iyayensu, a wata ganawa ta mussamam, tare da cewar na kusa za’a bayyana musu irin tsarin da aka fitar domin yaran.

 

Da yake gabatar da yaran , CSP Babagana Saje ya bayyana rahoton sace  wani yaro da aka yi ne har ta kai rundunar da gano ragowar wadannan yara da aka sace aka kuma sayar da su a jihar ta Anambra.

 

Ya ce tuni wadanda ake zargi wato matar da mijinta da suke aikata wannan laifi ke hannun hukuma wanda suke sayar da su akan kudi naira dubu darri biyu ga wata mata a Onitsa dake jihar ta Anambra, wanda ita kuma take sayar wa wata mata a jihar Lagos, wanda aka gano yara biyu a hannunta da ake bautar da su ta hanyar ayyukan gida.

 

A dai cikin yaran ne kuma aka gano guda biyu da tuni suka koma addinin Krista domin an boye asalinsu da inda suka fito.

 

CSP Babagana ya ce daga cikin yara tara, guda bakwai daga cikinsu an sami iyayensu bayan dogon bincike biyu kuwa har kawo yanzu ba’a sau iyayensu ba.

 

Malam Muhammad Ali wanda daya daga cikin wanda aka sace ‘yarsa ya ce tun shekara ta 2016 ne aka sace yarsa Aisha , inda yake cewa yana cike da farin ciki da godewa rundunar yan sandan Najeriya da ta gano masa yarsa da ya dade yana nemanta.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!