Labarai
Ana zargin likita da sanadin mutuwar mara lafiya
Ana zargin asibitin WISDOM mai zaman kansa a Nassarawa GRA da yiwa wani mara Lafiya tiyata tun kafin sakamakon da zai nuna za’a iya yi masa aikin ko kuwa a’a ya fito.
Daya daga cikin ‘yan uwan marigayi mai suna Bashir Hassan ya ce mamacin na fama da ciwon sukari ne wanda ya taba masa kafa har ta kai sai an yanke ta, don haka aka tura su su yi gwajin jini da sauran gwaje-gwajen da zasu nuna cewa za’a iya yi masa aikin ko kuma a’a.
Amma sun tafi yin gwaje-gwajen kafin su dawo sai suka tarar sun yi masa aikin har ya rasu likitan kuma ya Gudu.
AKTH ya samu nasarar gudanar da aikin kwakwalwa karo na biyu
Gwamnatin tarayya ta shaidawa ma’aikatan lafiya muradinsu ba mai yiwuwa bane
‘Yan uwan mamacin sun kuma sheda cewar saida suka bukaci su ajiye Naira dubu dari da Ashirin 120’000 a matsayin kudin kafin alkalami.
Yayin da suka nemi su bada Naira dubu tamanin 80,000 hukumomin asibitin suka ki saida su basu gaba ki daya.
Ko da muka tuntubi Shugaban asibitin Dr, Ujudu Pitters ya ce yanzu ana kan buncike ba zai ce komai ba kan batun.