Siyasa
Muna rokon gwamna Ganduje ya sulhunta Muntari da Sha’aban –Habib Sadam

Daya daga matasan ‘yan siyasa na karamar hukumar birni da kewaye Habib Sadam Makwarari ya roki gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da ya sasanta manyan bangarori biyu na jami’iyyar APC a karamar hukumar.
A cikin shirin Kowane Gauta na nan Freedom Radio Habib Sadam ya bayyana cewa
“Ni dan karamar hukumar birni ne gaba dayan su ba inda babu dan uwana, ko ta auratayya ko ta musulunci ko ta zamantakewa, ba wanda ba dan uwana ba a ajiye maganar siyasa, wannan maganar za ta iya haifar mana da da mara ido”
Ya kara da cewa dukkan bangarorin dake da sabani da juna ‘yan uwana ne kuma ko babu siyasa cikin su za mu koma, a don haka yake rokon gwamnan ya yiwa Allah da ma’aiki ya shiga tsakanin bangarorin domin gudun kada rikicin ya rikide ya koma kan mallam talaka a cewar sa.
Rubutu masu alaka:
Dokar tsaftacce soshiyal midiya ba zata yi tasiri ba – Aminu Mai dawa
Muntari Ishaq ya can-can ci zama kwamishina -Aminu Mai dawa
Sharhi
Rikicin Aisha Buhari da mukarraban Shugaban kasa: Yaushe wuta zata tsagaita?

Tun a shekarar 2016 ne uwargidan shugaban kasa Aisha Muhammadu Buhari ta fara bayyana rashin jin dadin ta game da wadanda ta bayyana ’yan bani na iya suka hana ruwa gudu a gwamnatin da mijinta kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ke jagoranta.
Aisha Buhari wacce a yanzu shekaru talatin kenan da suka yi aure da shugaban kasa Muhammadu Buhari bayan rabuwar da yayi da marigayiya tsohuwar uwargidan sa Hajiya Safinatu ta cigaba da kin boye abunda ke damun ta game da yadda wasu ke katsalandan a tafiyar da al’amuran na Najeriya.
Masu sharhi akan al’amuran yau da kullum sun banbanta akan irin yadda maidakin na shugaban kasa ke bayyana ra’ayinta a game da tafiyar da gwamnati da shugaba Muhammadu Buhari ke yi , inda wasu ke ganin cewa tayi dai dai da bayyana rashin jin dadinta da kuma kokarin kawo gyara.
Amma wasu na ganin duba da yadda al’ada da addinin mutanan arewacin kasar nan yake, bai kamata Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta rika bayyana gazawar mijinta a kafafan yada labarai ba domin ita mace ce da ta ke da aure wanda matan musulmi basa bayyana a bainar jama’a sai hakan ya zama dole.
Ko a shekarar 2016 da Aisha Buharin ta nuna cewa wasu ne suka karbe ragamar mulkin Najeriya suke yin abunda suke so , bayan bayyanar bayanan nata a kafar yada labarai ta BBC sai da aka tambayi shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa yaya zai bayyana mai dakinsa.
Tunda cikin harshen turanci ya bayar da misalin sai shugaba Buhari yace shi dai abunda ya sani tsakanin sa da mai dakin sa shi ne tana dakinsa da gurin dafa abinci da kuma wani dakin daban.
Hakan yasa jama’a da dama suka rika mamakin na martanin da Shugaba Muhammadu Buhari ya mayar akan caccakar da matar sa tayi wa gwamnatin ta sa.
Duk da haka tun fara dambarwar ,Shugaba Muhammadu Buhari bai taba mayarwa da Aisha Muhammadu Buhari martani akan caccakar da take yi na salon tafiyar da mulkin nasa ba.
Tun sanda ta fara ganin al’amura basa tafiya daidai a gwamnatin ta Shugaba Buhari wanda ita Hajiya Aisha take ganin talakawa ne suka sha wahala wajen samun nasara amma wasu ‘yan tsiraru suka mamaye da karbe iko kuma take ganin cewa talakawan basu amfana ba ko kadan.
Akwai ma wasu lokuta da Hajiya Aisha Buhari ta bayyana cewa asibitin dake fadar shugaban kasa babu cikakkun kayan aiki da zai kula da marasa lafiya ballantana sauran asibitocin kasar nan.
Tarihin bayyanar Aisha Buhari
‘Yan Najeriya sun fara ganin Aisha Muhammadu Buhari ne a zaben shekarar 2015 lokacin da shugaba Buhari ya amince da ta shiga yakin neman zaben sa .
Amma da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito takarar shugaban kasa a shekarar 2003 da 2007 da 2011 ’yan Najeriya da dama da kuma magoya bayan shugaban basu san Aisha Muhammadu Buhari ba har sai lokacin zaben shekarar 2015.
Abunda ya bullo a satin nan
Kwatsam a ranar larabar da ta gabata sai ga shi uwargidan shugaban kasa ta zargi mai taimakawa shugaban kasa Muhammadu Buhari na musammman akan harkokin yada labarai da fuska biyu wajen gudanar da ayyukan sa.
Aisha Buhari ta bayyana cewa Malam Garba Shehu yana bin umarnin Mamman Daura ne ba na mijinta ba.
A zargin da tayi tace Mamman Daura ya umarci Garba Shehu da cire ‘’yan jaridun da suke aiki a ofishin mai dakin shugaban kasa da aka fi sani da First lady.
Yaushe rikicin zai tsagaita?
Har ya zuwa yanzu babu wani bangare a fadar Shugaban kasa ko shi Malam Garba Shehu ko Mamman Daura da ya mayar da martani.
Ko wane dabaru shugaba Buhari zai dauka na takaita maganar da ta shafi tafiyar da mulki da maidakin sa take yi ga manema labarai a shekaru uku da suka wuce.?
Siyasa
Dai-dai ne kalaman Aisha Buhari –Shamsu Kura

Wani dan siyasa a jihar Kano mai suna Shamsu Kura ya bayyana cewa kalaman da uwar gida shugaban kasa Aisha Buhari tayi gaskiya ne, domin kuwa batune da suka jima suna fadawa duniya cewa shugaban kasa ba shi ne yake mulkin kasar nan ba.
Yayin zantawarsa da Freedom Radio ta cikin shirin Kowane Gauta na ranar Larabar da ta gabata Shamsu Kura ya ce talakawan Nigeria Buhari suka zaba ba Mamman daura ko Garba Shehu ba.
A wannan makon da muke ciki ne dai uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta aike da wata wasika ga jaridar Daily Trust wadda aciki ta bayyana cewa malam Garba Shehu da Mamman Daura suna yin shish-shigi a cikin ayyukan shugaban kasa.
Aisha Buhari ta ce Garba Shehun yana yin katsalandan hatta acikin al’amuran da suka shafi shugaban kasa da iyalansa, koda rufe ofishin matar shugaban kasa Mamman daura ne yabawa Garba Shehu umarni bawai umarnin shugaban kasa bane a cewar Aisha Buhari.
Labarai masu alaka:
Aisha Buhari ta nemi gafarar ‘yan Najeriya
Siyasa
Dokar tsaftacce soshiyal midiya ba zata yi tasiri ba – Aminu Mai dawa

Fitaccen dan siyasar nan Alhaji Aminu Maidawa Fagge ya bayyana cewa ko kadan dokar tsaftace shafukan sada zumunta da gwamnati tayi ko kadan ba ta magance komai ba.
Maidawa ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Kowane Gauta na nan Freedom Radio inda ya bayyana cewa ga hukumomi nan irin su EFCC an kafa su da kyaky-kyawar niyya amma yanzu sun koma aiki ga wani bangare guda daya.
Sannan ya kara da cewa za’a iya yin amfanin da wannan doka wajen hana masu adawa da gwamnati damar bayyana kura-kuran da gwamnati ke tafkawa.
Rubutu masu nasaba:
Shariar Ganduje da Abba: Jamiyyar PDP na zargin sauya Alkalai
Muntari Ishaq ya can-can ci zama kwamishina -Aminu Mai dawa
-
Labaran Kano6 months ago
Sarki Muhammadu Sunusi II ya amsa takardar tuhumar da gwamnatin Kano ke masa
-
KannyWood2 months ago
An fara sulhu tsakanin jaruman da suka yi auren mutu’a
-
KannyWood2 months ago
Abinda yasa ‘yansanda suka cafke Sadiya Haruna
-
KannyWood2 months ago
Abinda ya sanya ba zan iya auren Yawale a zahiri ba -Rayya
-
KannyWood2 months ago
Yadda akayi auren mutu’a a Kannywood
-
Labarai2 months ago
An garkame Sadiya Haruna a gidan yari
-
KannyWood2 months ago
Kun san abinda ya hana jaruma Maryam Yahya aure?
-
Manyan Labarai2 months ago
An gano wanda ya fito a bidiyon da ake zargin Daurawa ne