Connect with us

Labarai

Kano9: Har yanzu akwai yara sama da 90 da ba’a gano ba -inji iyayen yaran

Published

on

Kungiyar iyayen yara da aka sacewa yara ta jihar Kano ta ce har yanzu akwai sama da yara casa’in da daya da masu satar yara suka sace a wasu daga cikin unguwannin jihar Kano.

Shugaban kungiyar na jihar Kano Isma’il Ibrahim Muhammad ne ya bayyana hakan a yau lokacin gudanar da addu’oi’n neman taimakon Allah ya bayyana musu sauran ‘ya’yansu da masu satar yara suka sace a jihar Kano.

Ismail Ibrahim ya kara da cewa cikin unguwannin da satar kananan yaran tafi kamari akwai unguwar Hotoro, Kawo, Yankaba da sauran unguwanni, a don hakane suke kira ga gwamnati da ta kara kaimi wajen an gano musu sauran ‘ya’yansu da aka sace.

Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya rawaito cewa manyan malamai da dama ne suka halarci taron addu’ar da iyayen yaran da aka sace da kuma sauran al’ummar gari.

Labarai masu alaka:

Kano9: Karanta cikakken labarin yaran Kano da aka sace

Kano9: Al’umma suna ta karrama kwamishinan ‘yan sanda sakamakon ceto yaran Kano

Kano10- An sake ceto wani yaro daga jihar Anambra

Labarai

 Zulum sarkin aiki – Inji masu iya magana

Published

on

Daga Nasiru Salisu Zango

farfesa Babagana Umara Zulum shine Gwamna da yanzu ya zama zakaran gwajin dafi a cikin gwamnonin Nigeria.
Kokarinsa da jajircewarsa wajen kare hakkin talaka a salon mulki irin na salihan baya, shine ya zame masa Jari wajen samun karuwa, ba a jihar Borno Kadai ba har ma a Nigeria baki daya.

Gidan radiyon freedom muryar jama’a zai cigaba da kawo muku Shiri na Musamman akan ayyukan Professor Babagana Umara Zulum gwamnan jihar Borno.

za’a yi ne a tasoshin mu dake Kano da Kaduna.

Shirin zaizo da karfe 7.30 na dare a tashar freedom Kaduna, karfe 8 zuwa 10-10:30 na daren Lahadin a tashar Freedom dake Kano.

HON. Tanimu Tahir Mbaya mataimakin gwamnan jihar Borno a Fannin Yada labarai shine ya dauki nauyin kawo shirin.

A kasance damu Dan Jin kokarin Murucin Kan Dutse Bai fito ba sai da ya shirya.

Rubutu daga Nasiru Salisu Zango

Continue Reading

Labarai

NAHCON ta karrama tashar Freedom Radiyo

Published

on

Hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON ta karrama wakilin Freedom Radio a jihar Kaduna Abubakar Jidda Usman matsayin Dan Jarida mafi kwazo wajen kawo rahoton aikin hajjin da ya gabata.

A yayin wani bikin karramawa da kungiyar masu aike da rahotanni na aikin hajji masu zaman kan su suka shirya a birnin tarayya Abuja an baiwa hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano lambar yabo kan hukumar da tayi fice wajen kula da kayan alhazai.

Kazalika an karrama hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kaduna matsayin wadda tayi fice wajen shirya aikin hajji.

Haka kuma an bada lambar yabo ga hukumar jin dadin alhazai ta birnin tarayya Abuja matsayin wadda tayi fice wajen samar da kyakykyawan masauki.
Sauran jihohin da suka samu lambobin yabo sun hada da Yobe, Kwara da kuma jihar Niger.

Continue Reading

Labarai

Zamu yi aiki tare da hukumar kiyaye hadura ta kasa dake Kano- Haroun Ibini Sina

Published

on

Hukumar Hisbah ta  jihar Kano ta kai ziyara ga hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa a jiya Laraba

Babban kwamandan hukumar Hisbah Sheikh Muhammad Haroun Ibini Sina ne ya jagoranci tawagar hukumar Hisba don kai ziyarar.

Kazalika hukumnar ta Hisba ta nemi hadin kai domin yin aiki tare da jami’an hukumar kiyaye afkuwar haduran don ciyar da al’ummar jihar Kano gaba.

Da yake jawabi shugaban hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa shiyyar Kano Zubairu Mato wanda ya karbi tawagar ta hukumar Hisbar ya nuna farin cikin matuka da wannan ziyara aiki.

Har ila yau Zubairu Mato yayi alkawarin cewa hukumar su zata yi aiki kafada-da-kafada da hukumar Hisbah musamman wajen lura da sanya idanu ga masu amfani da ababan hawa domin tabbatar da zaman lafiya ga al’umma baki daya.

 

 

Continue Reading

Now Streaming

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!