Connect with us

Labaran Kano

Gwamnatin tarayya za ta samar da wuta mai amfani da hasken rana

Published

on

Ministan wutar lantarki na kasa Injiniya Sale Mamman, ya ce akwai bukatar samar da karin manyan dama -damai da za su kara inganta harkar samar da wutar lantarki a kasar nan.

Injiniya Sale Mamman na bayyana hakan ne yayin zantawar sa da gidan radiyo freedom kan cika shekaru dari da yayi a ofis na irin ayyukan da ya gabatar a ma’aikatar.

Ya ce ana sa ran samun wutar lantarki mega watt dari bakwai a tafkin Shiroro da na kainji, wanda a yanzu da kyar ake iya samar da mega watt dari hudu, hakan na daya daga cikin kalubalen da ke kawo koma baya a sha’anin wutar lantarki a kasar nan.

Ya kuma ce ma’aikatar wutar lantarki sun dukufa wajen ganin ta ci gaba da samar da wutar lantarki yadda ya kamata musamman ta hanyar hasken rana da iska.

Sale Mamman ya kuma ce duba da rashin ishashiyar wutar lantarki da ake samu a Arewacin kasar nan ne ya sanya ma’aikatar za ta samar da Karin tashohin wutar a nan Arewa musamman a jihar Kano dan inganta masana’antun dake yankunan.

Injiniya Sale Mamman ayayin tattaunawar ya kuma ce, manyan kamfanonin dake karbar wutar dan rabawa ga al’umma suna daya daga cikin wadanda ke kara ta’azzara rashin wuta a kasar nan ta yadda idan an turo wutar basa iya karba dan rabata ga jama’a.

Ya kuma ce kamfanonin dake raba wutar a kasar nan sunfi so sukai ta zuwa unguwannin da suke biyan su kudade masu Asoka ko kuma kamfanoni, ta yadda ta hakan ne kadai suke iya samun kudade masu yawa.

Injiniyya Sale Mamman ya ce jihohi da dama a kasar nan da dama basa iya biyan kudin wutar da suka karba, inda ya buga misali da jihar Lagos da cewa bata iya biyan kashi daya cikin hudu na kudin wutar da ake bata a duk wata.

Shugaban ya ce hanya da ya ce za’a iya bi dan magance matsalar rashin samun ishashiyar wutar lantarki ,ita ce samar da mitoci a gidaje ta yadda kowa zai iya sanin wutar da yake sha, suma masu kamfanonin su samu saukin karbar kudaden wutar a hannun al’umma.

Inda ya ce ma’aikatar ta na nan ta na gudanar da tsari ta yadda za ta sanyawa kowanne gida da shaguna da kamfanoni mita yadda kowa zai dinga sanin wutar da yake sha kuma za’a sanya mitocin ba ko sisin mutun ta yadda za’a dinga cire kudin mitar ahankali har mutun ya gama biya.

Ya ce yanzu ma’aikatar na nan na duba yiwuwar samun masalaha tsakanin masu karbar wuta da masu rabata yadda za’a samu ingantacciyar wuta musamman yadda za’a cigaba da samun cigaban tattalin arzikin da ya kamata.

Injiniyya Sale Mamman ya ce ma’aikatar na nan na kokarin shigo da tsarin da zai baiwa kananan ‘yan kasuwa wutar lantarki suna sayar da ita ga al’umma ta yadda wadanda ke bukatar wutar da yawa za su dinga samunta yadda ya kamata dan saukaka musu aiyuukan su da cigaban tattalin arzikin su.

Ko da aka tambaya shi wasu kasashen da ke makwabtan da kasar nan ke samun wuta awanni ashirin da hudu batare da daukewa ba kuma suna samun wutar ne daga nan Najeriya sai ya ce kasashen na biyan kasar nan kudin wuta yadda ya kamata sabanin yadda abin yake a nan gida Najeriya.

 

Continue Reading

Labaran Kano

An bukaci a daga darajar kwalejin ilimi ta Nasiru Kabara zuwa jami’a

Published

on

Dan majalisar dattijai mai wakiltar yankin Kano ta Kudu Sanata Barau Jibrin ya bukaci shugaban darikar kadiriyya ta Afrika Sheikh Kariballah Sheikh Nasir Kabara da ya daga darajar kwalejin ilimi ta addinin musulunci da ya fara ginawa zuwa jami’a.

Dan majalisa Barau Jibrin ya bayyana hakan ne a wajen bikin Maukibi da mabiya darikar Kadiryya suke gudanarwa duk shekara da aka gudanar a yau.

Sanata Barau Jibrin ya ce abin alfahari ne yadda aka fara samun mutane irin su Sheikh Kariballah da suke da kishin ilimin addinin musulunci suna irin wannan yunkuri na bunkasa addinin musulunci, a don haka ne shima yayi alkawarin rubanya aikin ginin har sau uku matukar aka daga darajar kwalejin zuwa jami’a.

Barau Jibrin ya kuma ce matasa na matukar bukatar irin wadannan jami’o’I na addinin musulunci don kaifafa kwakwalwar su, kan ilimin addinin musulunci da kuma harkokin kimiyya da fasaha

Sanata mai wakiltar kudancin Kano ya kuma nuna takaicin sa kan yadda ake da jami’o’in addinin musulunci biyar kachal a Najeriya a lokaci guda kuma ake da na addinin kirista guda 34, yana mai cewa akwai bukatar al’ummar musulmi su dage wajen gina jami’o’in addinin musulunci.

Continue Reading

Labaran Kano

Sulhu tsakanin al’umma zai rage cunkoso a kotuna

Published

on

Wata kungiya mai rajin ganin an tabbatar da gaskiya da adalci dake garin Kumbotso, ta ce samar da kungiyoyin al’umma da zasu dinga aikin sulhunta jama’a zai taimaka wajen rage yawan yadda ake shigar da kararraki gaban jami’an tsaro da ma masu unguwanni a jihar Kano.

Shugaban kungiyar Isyaku Ahmad ne ya bayyana hakan ta bakin sakataran kungiyar dake kula da tsare-tsare Iliyasu Nuhu, yayin taron jin ra’ayin jama’ar garin na Kumbotso kan ayyukan da kungiyar ta sanya a gaba.

Ilyasu Nuhu ya ce a yanzu ana yawan samun shigar da kararraki gaban jamian tsaro kan dan abinda za’a a iya magance shi ta hanyar sulhu, amma sai batun ya yi zafin da har sai anje gaban kotu, yana mai cewa hakan na taka rawa wajen samar da cunkoso a gaban kotuna.

Wasu daga cikin mahalartar taron sun bayyana cewa wannan sabon tsarin zai taka rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kuma fahimtar juna tsakanin al’ummar yankin.

Wakilin mu Abubakar Tijjani Rabi’u ya ruwaito cewa taron ya samu halartar shugabannin addinai daban-daban da kungyoyin kare hakkin dan adam dana yaki da cin hanci da rashawa da sauran al’umma.

Continue Reading

Labaran Kano

Ku kasance masu yin kasuwanci kamar yadda addinin musulunci ya koyar

Published

on

An shawarci ‘yan kasuwa da sauran ma’aikata da su kasance masu gudanar da harkokin kasuwancinsu irin yadda  addinin musulunci ya koyar domin kaucewa fadawa cikin fushin ubangiji a ranar gobe kiyama.

Shugaban cibiyar koyar da zaman Aure da kasuwanci a addinin Musulunci Dakta Yahya Tanko ne ya bayyana hakan yau lokacin taron bita tare da wayar da kan ‘yan kasuwa da ma’aikata kan tarbiyyar addinin musulunci a cikin harkokin kasuwanci.

Ya kara da cewa abin takaici ne yadda ‘yan kasuwa a yanzu suke gudanar da harkokin kasuwancin su, wanda hakan ya sauka daga layin koyarwa irin ta addinin musulunci.

A cewar Dakta Yahya Tanko kamata ya yi duk wani musulmi a ko ina yake ya zama tamkar mudubi da kowacce al’umma zata rika koyi da shi ta fuskar kasuwanci.

Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito cewa malamai da ‘yan kasuwa da ma’aikata da dama ne suke halarci taron.

Continue Reading

Now Streaming

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.