Labarai
Sarkin Kano ya bude masallacin juma’a na sabuwar jami’ar Bayero
Mai mairtaba Sarkin Kano Malam Muhammad Sunusi na biyu ya jagoranci bude sabon masallacin juma’a na sabuwar jami’ar Bayero dake Kano.
Da yake gabatar da hudubar juma’a a masallacin, Malam Muhammad Sunusi na biyu ya bayyana dumbin ladan da mahalicci ya tanada ga masu gina Masallatai da kuma masu hidimatawa masa a ko wani irin yanayi.
Da yake jawabi a wajen taron bude masallacin, shugaban jami’ar Bayero dake Kano Farfesa Muhammad Yahuza Bello, jan hankalin al’umma ya yi da su zama masu kokarin ganin an tsaftace masallatan juma’a da ma sauran al’amuran da za su inganta masallatan.
Babban limamin Kano Farfesa Sani Zahraddeen wanda shine shugaban kwamitin Masallacin, ya godewa wadanda suka ba da gudunmawa wajen samar da Masallacin juma’ar na sabuwar Jami’ar ta Bayero.
Wakilinmu na fadar Sarkin kano Muhammad Harisu Kofar Nasarawa ya rawaito cewa mai martaba Sarkin Kano Muhammudu Sanusi na biyu ya jagoranci dimbin al’ummar Musulmi sallar Juma’a a sabon Masallacin na Sabuwar Jami’ar Bayero a nan Kano.