Connect with us

Labarai

Sarkin Bichi ya jagoranci sallar Juma’a

Published

on

Maimartaba Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero ya jagoranci sallar Juma’a ta yau, a babban masalacin juma’a na garin Bichi bayan da ya isa fadar sa da safiyar yau.

Jaridar Kano Focus ta rawaito cewa a ya yin hudubar Sarkin Bichi yayi kira ga al’umma da su rinka taimakawa ‘yan uwan su a koda yaushe.

Kazalika ya yi kira ga ‘yan uwa musulmai da su tuba izuwa ga Allah kasancewar ubangiji na karabar tuba a koda yaushe.

Alhaji Nasiru Ado Bayero ya ce taimakon juna a tsakanin al’umma na cikin halaye kyawawa na manzon tsira Annabi (S.A.W) a don haka ya bukaci al’umma kan su rika taimakon juna.

Karin labarai:

Manyan abubuwa 4 da hudubar da Muhammadu Sunusi II ta kunsa

Sarkin Kano ya bude masallacin juma’a na sabuwar jami’ar Bayero

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 334,763 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!