Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kungiyoyin manoma ku biya bashin da ake bin ku -CBN

Published

on

Babban bankin kasa CBN ya yi kira, ga Kungiyoyin manoman Auduga wadanda suka cigajiyar samun bashi na tsarin shirin bada rance ga manoma da su yi kokarin dawowa da bankin rancen da suka karba, domin baiwa sauran manoma damar karbar wani bahi a nan gaba.

Shugaban Bankin a nan Kano Alhaji Ali Abdulkadir ne ya bayyana hakan yayin taron da kungiyar Manoman Auduga ta kasa shiyyar Kano ta shirya na kaddamar da fara karban biyan bashin da aka baiwa manoman a shekara ta 2019.

Alhaji Ali Abdulkadir ya kara da cewa kamata yayi manoman su ji tsoron Allah su dawo da rancen da aka basu domin an tsara shirin ne domin tallafawa harkar noma tare da bunkasa shi domin ci gaban manoma a kasar nan.

Za’a dawo da ma’aikatun casar Shinkafa a Kano -Nanono

RIFAN: ta bayyana matakan da manoma za su karbi bashi

EFCC shipyard Sokoto ta kama shugaban kungiyar manoman shinkafa na karakamar hukumar Gumi

Da yake jawabi a yayin taron Alhaji Sai’du Dattijo Adahama cewa yayi babban abunda ke ci wa masu kamfanonin masaku  tuwo-a-kwarya anan Kano shi ne bai wuce rashin aiwatar da bukatarsu a majalisar dokoki ta Kano ba wajen siyan kayayyakin da suke noma maimakon shigowa da shi daga kasashen waje, amma yaci tura.

Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito cewa mambobin kungiyar manoman Auduga da dama ne suka halarci taron daga ko ina a kananan hukumomin jihar Kano 44 domin biyan bashin da suka karba daga wajen bankin na CSN.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!