Labarai
Mun fara aiki kan masu Keke da babura -KAROTA
Hukumar lura da zirga-zirgar ababan hawa ta jihar Kano KAROTA ta bayyana cewa a yanzu haka tuni ta mayar da hankali kan babura masu kafa biyu, sakamakon irin dokokin ta da suke ketawa akan titi.
Shugaban hukumar KAROTA Baffa Babba Danagundi ne ya bayyana hakan a yau Litinin yayin da yake jawabi ga kungiyoyin masu baburan adai-daita sahu a shalkwatar hukumar dake nan Kano.
Baffa Babba ya ce tuni masu baburan adai-daita sahu sukayi biyayya ga dokokin KAROTA “domin a yanzu mafi yawa masu babura mai kafa uku basa haura layi akan titi.
An cafke direban da ake zargin yayi sanadin mutuwar jami’in KAROTA
Haraji: Mun rage Adaidaita Sahu zuwa dubu dari- KAROTA
Sai dai babura masu kafa biyu a don haka tuni na bada umarni daga yau dinnan a fara aiki na musamman kan matuka babura mai kafa biyu da masu Keke da suke karya dokokin mu” a cewar Baffa Babba.