Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Wa kuke ganin zai zama zakaran kwallon kafa na nahiyar Afrika a bana?

Published

on

A yau ne hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF zata fitar da sunaye ‘yan wasan da suka fi bajinta a kwallon kafa a shekarar 2019 da muka yi ban kwana da ita.

A taron bayar da kyautar wanda zai gudana a kasar Masar, za’a bayyana gwarzon dan kwallon kafa a bangaren maza da gwarzuwar ‘yar kwallon kafa a bangaren mata.

Sai matashi da matashiyar ‘yan wasa a bangaren maza da mata, da kuma gwarzon mai horas da ‘yan wasa na maza dana mata.

‘yan wasa 3 da za’a zabi gwarzo a bangaren maza sune Riyad Mahrez da Sadio Mane da Muhammad Salah.

Riyad Mahrez ya taimakawa kungiyarsa ta Manchester City lashe gasar Firimiyar kasar Ingila, inda daga bisani ya jagoranci kasar sa ta Algeria lashe gasar cin kofin Afrika ta shekarar 2019 bayan da ya taka rawar gani a gasar, ciki kuwa har da kwallon da ya ci Nijeriya a bugun tazara a wasan kusa dana karshe na gasar, wanda hakan ya taimakawa Algeria zuwa wasan karshe tare da lashe gasar karon farko cikin shekaru 29.

Duk da ya kasa jagorantar kasar Senegal lashe gasar cin kofin Afrika na 2019 inda suka yi rashin nasara a wasan karshe a hannun kasar Algeria da ci daya mai ban haushi, Sadio Mane ya samu nasarar shiga cikin jerin ‘yan wasa 3 da za’a zabi gwarzon dan kwallon kafa na Afrika. Mane ya zura kwallaye 34 tare da taimakawa aka zura kwallaye 12 a shekarar ta 2019 wanda hakan ya taimakawa Liverpool lashe gasar cin kofin zakarun nahiyar turai.

Biyo bayan taimakawa kungiyar kwallon kafa ta Liverpool lashe gasar cin kofin zakarun nahiyar turai, mai rike da kambun kyautar Muhammad Salah dan kasar Masar ya samu nasarar shiga cikin jerin sunayen. Muhammad Salah ya zura kwallaye 26 tare da taimakawa aka zura kwallaye 10 a wasanni 55 da ya fafata a shekarar 2019.

A bangaren mata ‘yar wasan gaba ta Nijeriya Asisat Oshoala wadda ke taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona dake kasar Spaniya, zata kara da Ajara Nchout yar kasar Cameroon daThembi Kgatlana yar kasar Afrika ta Kudu wajen lashe kyautar a bangaren mata.

A bangaren matasan ‘yan wasa akwai

Dan wasan Nigeria Samuel Chukwueze dake taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Villarreal dake kasar Spaniya.

Victor Osimhen dan Nigeria mai wasa a kungiyar kwallon kafa ta Lille dake kasar Faransa.

Achraf Hakimi dan kasar Morocco wanda ke wasa a kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund dake kasar jamus.

A bangaren masu horaswa na maza

Aliou Cisse na  Senegal

Djamel Belmadi na Algeria

Moïne Chaâbani na Tunisia

A bangaren masu horaswa na mata

Alain Djeumfa na Cameroon

Desiree Ellis na Afrika ta kudu

Thomas Dennerby na Nigeria

Tsawon shekaru ashirin Kenan rabon da dan wasan Nijeriya ya samu nasarar lashe kyautar gwarzon dan wasan afrika.

Kanu Nwankwo shine dan wasan kasar nan na karshe da ya samu nasarar lashe kyautar a shekarar 1999, inda ya doke dan wasan kasar Ghana mai tsaron baya Samuel Kuffour da dan wasan kasar Ivory Coast Ibrahima Bakayoko.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!