Connect with us

Labaran Wasanni

Dan wasan Najeriya zai iya lashe kyautar gwarzon Afrika

Published

on

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Sevilla dake kasar Spaniya Frederic Kanoute, ya ce dan wasan kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles Samuel Chukwueze, zai iya zama gwarzon dan wasan Afrika a nan gaba.

Kanoute wanda tsohon dan wasan kasar Mali ne, ya kuma taba zama gwarzon dan wasan Afrika a shekarar 2007.

Haka zalika Kanoute na daya daga cikin jakadun kwallon kafa daga Afrika a gasar Laligar kasar ta Spaniya.

Yanzu -yanzu an dage gasar wasanni ta kasa saboda barazanar Corona

Manyan labaran wasanni a Najeriya

Frederic Kanoute ya bayyan hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai kan yadda ‘yan wasan Afrika ke nuna gwazo a gasar laligar kasar ta Spain.

Inda nan take ya bayyana sunan dan wasan kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles dake wasa a kungiyar Villareal, Samual Chukwueze dana kasar Ghana Thomas Partey dake wasa a kungiyar kwallon kafa ta Atlentico Madrid a matsayin yan wasan dake da kwazo a gasar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!