Labaran Kano
Da sahalewar ‘yan kasuwar waya ta farm Center- KAROTA
Shugabancin kasuwar Sayar da waya ta Farm Center a nan Kano ya musanta zargin da wasu ‘yan kasuwar ke yi cewa akwai amincewa wajen gyaran hanya da Hukumar KAROTA ta gudanar tayi a ranar Asabar din data gabata.
Jami’in hulda da jama’a na kasuwar Jamilu Bala Gama ne ya bayyana hakan ga manema Labarai, yana mai cewa aiki ne da hukumar KAROTA ta saba gudanarwa a duk kasuwannin bIrnin Kano domin tsaftace hanyoyin jihar Kano.
Jamilu Bala Gama ya kuma kara da cewa yanzu haka shugabancin kasuwar ya samar da wasu gurare domin wadanda abun ya shafa su koma don gudanar da sana’oin su kuma kyauta domin tallafa musu.
Mai magana da yawun shugabancin kasuwar Jamilu Bala Gama yace mutane su fahimci cewa tun a baya an baiwa wadanda suka kafa runfunansu a bakin titi an basu wa’adin kwanaki tallatin dasu kwashe kayan su a don haka mutane su sani babu hadin bakin kowa.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito shugabancin kasuwar na kira ga ‘yan kasuwar dasu kasance masu biyayya ga shugabancin kungiyar domin ciyarda kasuwar gaba.