Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Gwamnatin Kano zata bunkasa tattalin arziki

Published

on

Gwamanatin jihar Kano ta ce zata yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta bunkasa tattalin arzikin jihar.

Kwamishinan kasuwanci Alhaji Shehu Na’Allah  ne ya bayyana hakan ta bakin babban sakataren ma’aikatar Dakta Lawan Shehu Abdulwahab a yayin karbar bakuncin kungiyoyin dillalan kayayyaki reshen jihar Kano a jiya.

Ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Bashir Habib Yahya ya sanyawa hannu, ta ce, tun a shekarar 2017 gwamnati ta fitar da tsare tsare wadanda za su taimakawa harkokin masana’antu.

Dakta Lawan Shehu Abdulwahab, ya kuma bukaci mambobin kungiyar da su kasance masu bin doka da oda kafin ci gaba da gudanar da tsarin da zai bunkasa kasuwancin su.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!