Labarai
Gwamnati ta dakatar da wasu daliban Sakandire a Kano
Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da wasu daliban makarantar sakandiren kimiyya da fasaha ta garin Dawakin Tofa, sakamakon tarzoma da suka gudanar a daren jiya Juma’a.
Shugaban hukumar kula da makarantun kimiyya da fasaha ta jihar Kano, Alhaji Ahmad Tijjani Abdullahi ne ya bayyana haka, yayin wata ziyara da ya kai makarantar a yau asabar.
Ya ce, sun dauki wannan matakin tura yaran ga iyayen su ne, domin basu damar gudanar da binciken kwa-kwaf kan dalilin faruwar lamarin.
Sai dai, ya ce, an tura daliban gida na tsawon mako daya ne kacal kafin a kammala binciken.
Karin labarai:
Daliban Sakandire sun yi zanga-zanga a Bauchi
An rufe wata makarantar sakandire a Kaduna
Rahotanni sun ce, a daren jiya juma’a ne wata rigima ta barke tsakanin shugabannin daliban makarantar da sauran dalibai, wanda sanadiyar haka aka lalata kadarori da dama a makarantar.
Bayanai sun ce, daliban wadanda suke a shekarar karshe sun kori shugabanninsu wadanda suka tsere zuwa cikin gari tare da kone kayayyakin su.
You must be logged in to post a comment Login