Labarai
Daliban Sakandire sun yi zanga-zanga a Bauchi
Wasu daliban makarantun Sakandire a jihar Bauchi sun gudanar da wata zanga-zangar lumana a yau Jumu’a.
Masu zanga-zangar dai sun karade tituna daban-daban na jihar Bauchi inda suke kokawa kan wani kudiri da ma’aikata ilimi ta jihar ta kawo.
Daliban na kukan cewa a yanzu gwamnatin jihar ta dakatar da biya musu kudin jarrabawar kammala makarantar Sakandiren da gwamnatocin jihohi suka saba biya a baya.
Wasu daliban da suka nemi a sakaye sunan su sun shaidawa Freedom Radio cewa idan gwamnati baya biya musu wannan jarabawar ba to babu shakka karatun su ya shiga wani hali da ba lallai ne ya iya dorewa ba.
Kalli wasu hotunan zanga-zangar:
Da yawa daga cikin daliban na kukan cewa iyayensu basu da karfin da zasu iya daukar nauyin biya musu jarrabawar.
Freedom Radio tayi kokarin jin ta bakin kwamishinan ilimi na jihar Bauchi Dakta Aliyu Usman Tilde kan wannan batu amma abin ya ci tura.
Labarai masu alaka:
KUST Wudil ta karawa dalibai kudin makaranta
Dalibai 30 ne suka koyi sana’o’in dogaro da kai a Wudil
You must be logged in to post a comment Login